DALILIN RUFE DAKIN TARO NA SERVICE TO HUMANITY DA HUKUMAR HISBAH TA JIHAR KATSINA TAYI
- Katsina City News
- 19 Apr, 2024
- 593
A RANAR TALATA 16 GA WATAN AFRILU 2024
Kafin Bukukuwan Karamar Sallah a jihar Katsina, Hukumar Hizbah ta fitar da Sanarwa cewa ta Dakatar da duk wasu Ayyukan Baɗala a fadin jihar Katsina.
Hukumar tayi Nazari cewa wadannan Ayyuka na Baɗala suna da alaƙa da matsalar rashin tsaro da jihar Katsina take fama da shi.
Hukumar ta gano cewa wasannin DJ da Gala (Galla Night) da Matasa keyi Ana Shaye-shaye na kayan maye a wajen wanda mafiya yawa kananun yara ne, da ake amfani da wannan damar don lalata masu Tarbiyya.
Kasantuwar haka yasa Hukumar Hisbah bata yi Ƙasa a gwiwa ba wajen ganin ta dakatar da wadannan abubuwa. A cikin Ikon Allah mutane sunji kira kuma sun bi Dokoki da Ƙa'idojin da Hukumar ta ɗora masu.
Kuma Hukumar Hisbah ta sanar cewa Ba wai Bukukuwa aka hana ba. Ana so ne duk wani wanda zai shirya wani biki ya tuntubi hukumar ta Hisbah da kuma tsare-tsaren sa, hukumar ta duba kuma ta tantance tare da bashi shawara yanda zai gudanar da Hidimarsa.
Mafiya yawa daga Al'ummar jihar Katsina sun bi kuma sun gudanar da abinsu lami lafiya, sai wasu tsiraru da suka kangare, bayan sanar dasu cewa Abinda suke so suyi ba zai yiyu ba, amma duk da haka suka kangare suka Aiwatar da abinda suka yi niyya.
Da farko sunyi nufin yin wasan a Filin wasan kwallon kafa na Muhammadu Dikko Hukumar Hisbah ta hana a yi a wajen tare da dalilan hanawar. Hukumar Hisbah bata hana wannan Baɗalar don masu saida abinci ko masu kasuwanci a wajen ba. Amma duk da haka mutane da basu sani ba sai aka ta yada cewa wai Hisbah ta hana 'Yan kasuwa kasuwancin su, kuma wannan ba gaskiya bane.
Bayan hukumar Hisbah ta hana su a nan Filin wasa na Muhammadu Dikko, sai suka tafi Dakin Taro na Service Humanity, wanda kowa yaga abinda ya faru a nan, inda sukai waƙe waƙe na cin mutunci da Zinace-zinace a wajen, kamar yanda hukumar ta samu bayanan sirri.
Wannan Dalili yasa Hukumar Hisbah ta dauki matakin hanawa ba wai don masu kasuwanci a wajen ba. Hukumar Hisbah tana bawa Al'umma Kariya ne, kuma mun tabbatar masu da cewa zamu iya sanya jami'an mu su kula da su su basu kariya ko babu komai za'a kula da Dukiyar 'Yan kasuwa don gudun wasu bata gari su far masu.
Kowa ya sani hukumar Hisbah hukuma ce da take kokarin samar wa matasa abin yi, amma a tare da haka ba yarda da shigewa karkashin wata sana'ar ba kuma ayi barna. Kowa yaga Bidiyon abinda su wadannan mutanen suka yi na cin mutuncin da cin zarafin Hukumar Hisbah da zage-zage da sauran su.
Wannan Dalilin yasa hukumar Hisbah tayi amfani da damar ta wajen garkame wajen Taron kasantuwar su masu wajen sun san da wannan Dokar kuma Doka ta samar da mu, munce a bar wannan abin yaci karo da Dokar Hisbah, amma basu bari ba. Don haka mun rufe wajen saboda sun ki bin Doka da Oda, sun bari bata gari sunyi amfani da wajen su. Wannan yasa muka rufe wajen taron har sai mun gama bincike sana mu tabbatar da cewa ko sa iya bude wajen su, idan zasu bi Ƙa'idojin hukumar, da Dokokin ta, wanda Gwamnatin jihar Katsina ta kafa.
Don haka hukumar Hisbah ta jihar Katsina ba wai tana so a dunga laifi don ta kama mutane bane, manufar shine adaina laifin don bata so ta kama kowa. Saboda haka Hukumar Hisbah tana kira ga duk masu Ayyukan Assha ko aikin Baɗala da suji tsoron Allah su daina. Yin haka zai samar masu da zaman lafiya da Albarkar rayuwa a wajen Allah (S.W.T) kuma zasu zauna lafiya da hukumar Hisbah domin babu wanda zai yi ba daidai ba a fili kuma hukumar Hisbah ta sani amma mu sanya masa ido. Bamu da wanda yake shafaffe da mai, bamu da gagarare, a gudanar da Dokokin hukumar da tsare-tsaren ta.
Gwamnan jihar Katsina bai kafa hukumar Hisbah don cutuwa ko takurawa Mutane ba, sai don damuwa da irin halin Tabarbarewa tarbiyya da matasa suke ciki.
Muhammad Aminu Usman PhD. (Abu Ammar)
Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta jihar Katsina
19/4/2024