Yanda Sana'ar Kayan Nauyi ke Kyankyashe Kananun Ɓarayi a Katsina.
- Katsina City News
- 17 Apr, 2024
- 572
....Maƙabartu sun shiga Uku
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Sana'ar Kayan Nauyi Ko (Gwangwan) tana ƙara haifar Kananan Ɓarayi a jihar Katsina.
Binciken Katsina Times ya gano yara masu kananan shekaru da basu gaza goma zuwa Sha biyar ba, suka shiga sana'ar, amma mafiya yawa ba suna siya su saida bane, a'a suna farawa daga fara tsintar karafa a cikin Bola, zuwa lungunan unguwanni, daga nan kuma sai su karkata zuwa sata.
Ma'ana idan sun ga wasu karafuna a gida ko a bisa hanya wanda daukar su, sunan sa Sata a ma'anar ta, sai su balle ko su dauke.
Abin ya wuce satar kayan nauyin a cikin Unguwanni, har ta kaiga ana satar a cikin Maƙabartu.
Yanda suke yi kuwa shine, "Yaran suna shiga cikin Maƙabartu don ballar Allunan kabari da ke da alamar sunan mamaci da lokacin da ya Mutu, su fizge su gudu suje su saida.
"Mafiya yawa a Arewacin Nijeriya ana yiwa Maƙabartu Alama na Allon karfe da ke nuna sunan mamci da shekarar da ya rasu saboda 'ya'ya, 'yan uwa da sauran dangi su dunga kai ziyarar Addu'a."
A Makabartar Danmarna Makabarta mai Daɗaɗɗen Tarihi da aka Binne kusan duk wasu manyan mutane, Malamai, 'Yan Siyasa da Attajirai na Birnin Katsina da suka rasu, fiye da shekaru 400 zuwa yau, akwai Kaburbura da yawa dake dauke da alamar Allon, Amma yanzu sai dai sawu.
Katsina Times sun samu zantawa da masu gadin Makabartar inda suka gwada mana, yanda Barayin kayan nauyin ke shiga Makabartar suna balle karafan idan basu nan. Suka ce hatta kyaure na Makabartar ba a bari ba.
A cikin Makabartar ta Danmarna a kwai kebantaccen waje, da aka Binne Irinsu Baban tsohon shugaban Najeriya Marigayi Musa 'Yar'adua, Umaru Musa Yar'adua, Shehu Musa Yar'adua, Tsohon Ministan Gona, Abba Sayyadi Ruma, Malam Abba Saude, Shehu Shema (Mahaifin tsohon Gwamnan Katsina) Waziri Zayyad Rafin Daɗi, Maulaya Hassan, Alkalan garin Katsina da sauran Manyan Mutane, duka an fizge duk wata Alama da ke nuna kaburburan nasu.
"Idan da Akwatin Karfe ake Binne Mamaci dashi watarana idan muka zo sai mun iske mamaci bude a fili an cire akwatin an sace" inji wani mai gadin Makabartar da muka zanta dashi.
Mi hakan Zai haifar...?
Bayyane yake cewa kowa yaga yanda Matasa ke fadace fadacen kwatar karafa a wurare daban-daban inda gwamnati ke Ayyuka musamman gina Titi, ko wani abu da ya shafi rushewa da gina sabo, hakan har ya kaiga sare-sare a tsakanin matasan. Idan har wannan Mummunar dabi'a ta dore shakka babu zai haifar da Matsala da barazanar tsaro a cikin al'umma. Sana kuma goben matasa masu tasowa ba zatai kyau ba.
Mi Dilolin Sana'ar ke cewa:
"Bama sayen kaya wajen yara, sana kuma sai mun bincika mun tabbatar da inda suka fito, don ko wata alama muka gani da bamu natsu da ita ba, hakika mu ke rike yaro da kanmu ma mu hadashi da hukuma" inji wani mai san'ar Gwangwan da muka nemi jin ta bakinsa.