Yaya Karfin Sojan Iran Yake...?
- Katsina City News
- 14 Apr, 2024
- 1028
Ya ya karfin sojin Iran ya ke?
Duk da fuskantar takunkumin kasashen yamma na shekaru da dama, Iran har yanzu tana iya kasancewa daya daga cikin kasashe mafi karfi a Gabas ta Tsakiya da ke kan gaba zuwa 2024. an san sojojinta da karfin fada.
Girman rundunar sojin Iran
Iran na da sojoji kusan 523,000 a rundunoni daban-daban, kamar yadda cibiyar binciken dabaru na kasa da kasa da ke Birtaniya ta bayyana.
Kasar na da karin wasu dakaru 20,000 a rundunarta ta sojin ruwan dakarun juyin-juya halin Musulunci wato IRGC.
Rundunar ce ke yin sintiri da jiragen ruwan soji a mashigin Hormuz, inda aka yi ta artabu da jiragen mai na kasashe a shekarar 2019. IRCG ce kuma ke kula da rundunar sa-kai ta Basij da ke taimakawa wajen murkushe masu tayar da kayar baya a cikin kasar. Runudanar Basij na da dubban dakaru da ma'aikata.
Shekara 44 da suka wuce ne aka kafa runduar IRGC domin kare tsarin Musulunci a kasar. Rundunar ta samu ikon zama wani muhimmin bangare na harkokin soji da siyasa da tatalin arzikin Iran. Duk da karancin dakarunta idan aka kwatanta da rundunar tsaron kasar, ana ganin IRGC a matsayin sashen soji mafi karfin iko a Iran.
Aikin soji a kasashen ketare fa?
Bataliyar Quds wadda marigayi Soleimani ya jagoranta ce ke gudanar da ayyukan IRGC na sirri a kasashen ketare.
Bataliyar mai karfin soja 5,000 na gudanar da ayyukanta ne kai-tsaye karkashin jagoran addinin kasar wato Khamenei.
An tura wasu sojojin bataliyar a matsayin masu bayar da shawara ga sojojin shugaba Bashar al-Assad na Syria da mayakansa kan 'yan Shi'a da ke tare da su. A Iraki kuma rundunar ce ta taimaka wa jami'an tsaron farin kaya murkushe kungiyar IS da mayakanta. Amma gwamnatin Amurka na zargin ayyukan rundunar ya hada da samar da kudade da horo da makamai da kayan aiki ga kungiyoyin da Amurkan ke gani a matsayin 'yan ta'adda a Gabas ta Tsakiya. Kungiyoyin sun hada da Hezbollah ta kasar Lebanon da kungiyar jihadin Musulunci ta Falasdinu.
Matsaloli da takunkumin karya tattalin arziki sun kawo wa kasar tazgaro wurin sayo makamai. Kasar na da karancin makamai idan aka kwatanta da wasu kasashen yankin. Yawan makaman da kasar ta saya daga 2009 zuwa 2018 bai fi kashi 3.5% na makaman da Saudiyya ta saya a tsawon lokacin ba, a cewar cibiyar binciken zaman lafiya ta Stockholm..Galibin makaman tana sayo su ne daga Rasha, ragowar kuma daga China.
Shin Iran na da makami mai linzami?
Kwarai kuwa - makamai masu linzami da Iran ta mallaka shi ne babban karfinta na soji, duba da karancin karfinta na sojin sama idan aka kwatanta da manyan abokan gabanta irin Isra'ila da Saudiyya. Rahoton ma'aikatar tsaron Amurka ya ce Iran ce mafi karfin makamai masu linzami a Gabas ta Tsakiya. Makaman a cewar rahoton sun hada da masu cin gajere da kuma matsakaicin zango.
Amurka na ganin Iran na gwajin fasahar sama jannati ne domin kera makami mai linzami da ke iya keta tsakanin nahiyoyi ko ma fiye da haka. Iran ta dakatar da shirinta na makamai masu cin dogon zango saboda yarjejeniyar 2015 da ta kulla da wasu kasashe game da shirinta na nukiliya. Daga baya ta ci gaba da kera makaman sakamakon rashin tabbas da ke tattare da yarjejeniyar.
Duk da haka Iran za ta iya kai hari da makaman nata masu cin gajere da matsakaicin zango zuwa cikin kasar Isra'ila da Saudiyya da sauran kasashen yankin Gulf. A watan Mayun shekarar 2021 ne Amurka ta girke na'urar kakkabo makaman abokan gaba a Gabas ta Tsakiya sakamakon nuna yatsa tsakaninta da Iran.
Makamin na iya kakkabo jiragen yaki da rokoki da makamai masu linzami da abokan gaba suka harba a sararin samaniya.
A watan Yunin 2019 Iran ta kakkabo wani jirgin sintiri maras matuki mallakar Amurka bisa hujjar cewa ya keta hurumin sararin samaniyar kasar a mashigin Hormuz.
A 2019 wasu hare-haren da aka kai da irin jiragen sun lalata manyan matatun mai na Saudiyya guda biyu.
Amurka da Saudiyya suna zargin Iran da kai harin, amma ta musanta, inda ta dora laifin a kan 'yan Houthi na Yemen da suka dauki alhakin hare-haren.
Shin Iran na da fasahar intanet?
Bayan harin intanet da aka kai wa tashar nukiliyarta a 2010 kasar ta karfafa fasaharta ta intanet. Ana tunanin IRGC na da runduna ta musamman kan harkokin intanet da ke yi mata ayyukan leken aikin leken asirin kasuwanci da harkokin soji.
Rahoton da rundunar sojin Amurka ta fitar a 2019 ya zargi Iran da kokarin kaddamar da harin leken asiri ta intanet a kan kamfanonin tsaro da na jiragen sama da na makamashi da na albakatun kasa da na sadarwa a fadin duniya.
Shin Iran tana da makaman nukiliya?
Shirin nukiliya na Iran ya ci gaba amma Tehran ba ta da karfin makaman nukiliya a yanzu, yayin da ake daukar Isra'ila a matsayin kasa mai karfin makaman nukiliya da ba ta bayyana ba. Iran ta samu ci gaba sosai kan shirinta na nukiliya tun bayan ficewar gwamnatin Trump daga yarjejeniyar nukiliyar ta 2015.
Wane ne ya fi ƙarfin Iran ko Isra'ila?
Wani Rahoton ya ce kasafin kudin tsaron Isra'ila ya kai dalar Amurka biliyan 24.2, yayin da kasafi kudin tsaron Iran ya kai dala biliyan 9.9. Idan aka yi maganar jiragen yaki Isra’ila na da jirage 612, ita kuma Iran tana da jirage 551. Sai dai a bangaren tankunan yaki, Iran ta ninka Isra'ila kusan sau biyu. Isra'ila na da tankokin yaki 2200, ita kuma Iran tana da tankokin yaki 4071.
Yaya karfin sojojin saman Iran yake?
Babban raunin Iran shi ne sojojin sama. Yawancin jiragen kasar sun kasance tun zamanin Shah Mohammed Reza Pahlavi, wanda ya jagoranci Iran daga 1941 zuwa 1979, kuma da yawa sun lalace saboda rashin kayayyakin gyara. Kasar ta kuma sayi karamin jirgin ruwa daga kasar Rasha a shekarun 1990, in ji masana.