LAMIƊON KATSINA NA FARKO DA ALHERIN GIDAUNIYAR LAMIƊO
- Katsina City News
- 13 Apr, 2024
- 633
Mahmood Hassan
@ Katsina Times da Taskar labarai
Masarautar Katsina mai tsohon Tarihi ta ba da wasu muƙamai na sarauta a 'yan kwanakin nan. Daga cikin su akwai sarautar Lamiɗon Katsina, wanda aka bai wa Alhaji Jabiru salisu Tsauri a matsayin Lamiɗon Katsina na farko.
Masarauta tana ba da sarauta ne bisa dalilai daban, amma manyan dalilai suna iya kamawa guda uku. Na farko gado. Na biyu me ka yi wa al'ummarka. Na uku me za ka iya yi masu in ba ka?
Cikin wata ɗaya da ba Lamiɗon Katsina sarautar, har ya assasa Gidauniyar da ta taimaka wa al'ummar Katsina a watan Ramadan da ya gabata.
*Waye Jabiru SALISU Tsauri?*
An haife Jabiru Salisu ne a garin Tsauri da ke cikin ƙaramar hukumar Kurfi. Ya yi karatun addini a gida, ya kuma yi karatun boko har zuwa Jami'a.
Aikin farko da ya fara shi ne Malamin makaranta a makarantar sakandare da ke Malumfashi. Ya kuma taba zama ma aikaci a majalisar dake Abuja.
Ya fara shiga siyasa da tsayawa takarar Kansila a mazabar Tsauri A.
Lokacin da Alhaji Umar Ibrahim Tsauri ya zama Sanata sai ya ɗauki Alhaji Jabiru salisu a matsayin mai taimaka masa na musamman.
Bayan Sanata Tsauri ya kammala wa'adinsa, sai Sanata Ibrahim Idah ya ci gaba a matsayin sanata. Sai Jabiru Tsauri ya ci gaba da aiki da Sanata Idah.marigayi sanata kanti Bello shine ya bada shaida jabiru ga sanata idah.inda yace yaro mai Amana da kuma aiki tukuru, ya kuma San majalisar tarayya kamar bayan hannun shi.
Ya zama shugaban ƙungiyar masu taimaka wa sanatoci da 'yan majalisun tarayya na ƙasa. Wanda aka zabe shi da gagarumin rinjaye.
Bayan kammala wa'adin Sanata idah, Jabiru ya ci gaba da harkokin kasuwanci da kuma shiga harkokin siyasa a matakin gari da ƙaramar hukumarsa.
Lokacin mulki Malam Aminu Bello Masari, ya yi kantomomi a duk ƙananan hukumomin jihar Katsina, Jabiru Tsauri shi ne ya riƙe kantoman a ƙaramar hukumar Kurfi.
An rusa su bayan shekaru biyu, inda Jabiru ya ci gaba da harkokinsa na kasuwanci da shiga siyasa a matakin ƙaramar hukuma da kuma jiha.
Shi ne ya yi uwa ya yi makarbiya, na gaba-gaba na ganin Gwagwaren Katsina, Dakta Umar Raɗɗa ya fito takara. Da shi aka sawo fom, da shi aka mayar. Kusan kashi 99 na kamfen ɗin Dikko da shi aka yi.Ance suna tare da Dikko Radda na tsawon shekaru kafin siyasa da takara.
Bayan kafa gwamnati a watan Mayu, 2023, Gwamnan Katsina ya ba shi muƙamin shugaban ma'aikata a fadar gwamnatin jihar Katsina.
A kuma cikin shekarar nan ta 2024, Sarkin Katsina ya ba shi sarautar Lamiɗon Katsina na farko. Shi kuma ya kafa wata gidauniya mai suna gidauniyar Lamiɗon Katsina, wadda take ta ayyukan alheri a jihar, musamman yankin Katsina ta Tsakiya. Anyi ma gidauniyar shugabancin matakin jaha da na kananan hukumomi.
Sun ba da abinci a Katsina. Sun tallafa wa marayu da kayan Sallah. Sun ba da kuɗi ga marasa galihu.
GARIN TSAURI:
Lamiɗon Katsina ya fito daga wani gari ake kira Tsauri, wanda asalin sunansa Sauki, amma wani mayaƙi da ya yi suna mai suna Ɗanbaskore shi ne ya canza masa suna zuwa Tsauri.
Abin da ya faru shi ne, Ɗanbaskore mayaƙi ne da yakan zo daga ƙasar Maraɗin ta wancan lokacin. Yana cin birane da yaƙi, ya kama bayi ya kwashe masu dukiya.
Duk lokacin da ya zo mamaya garin Tsauri sai ya gagare shi shiga. Wani zuwa da ya yi sai kawai ya tare da mayaƙansa a kusa da wasu duwatsu. Yana mai cewa yau sai ya ga iyakar mutanen garin sauki.
Yana nan har kwanaki, sai kawai ya ga an harbo wata kibiya da ta zo sai ta fasa wani dutsi ta tsaya. Nan Ɗanbaskore ya tsorata, ya ce wannan gari ba a iya cin shi da yaƙi, kuma yanzu sunansa Tsauri, ba Sauƙi ba.
Tsauri gari ne mai tsohon tarihin sarauta da malantaka. Tun zaman Na Alhaji, ɗaya daga cikin waɗanda suka amso tuta wajen Sheikh Usman Ɗan Fodio (r.a) da kuma mayaƙa irin su Ɗan Waire.
Shekarun baya duk wanda za a ba sarautar 'Yandakan Katsina, sai ya riƙe sarautar Magaji Tsauri.
SARAUTAR LAMIƊO:
Ita wannan sarautar an aro ta ne daga masarautar Adamawa. A fassarar daga Hausa zuwa Fulatanci, tana nufin Jagora, ko Shugaba.koma sarki
Masarautun ƙasar Hausa sun saba aro sarautar wata masarautar su ba mutanen yankin su. Akwai sarautu da yawa da aka aro daga wasu wurare kamar Kano, Zaria, Borno da Sakkwato. Ana bayar da su a masarautar Katsina.
Sarautar Lamiɗo ta Fulani ce, kuma an aro ta ne daga masarautar Adamawa.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.taskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
All on All social media platforms
08057777762.07043777779
Email. newsthelinks@gmail.com
Katsinacitynews2@gmail.com