TATSUNIYA (4): Labarin Kura da Kurege. Kwaɗayi...!
- Katsina City News
- 07 Apr, 2024
- 613
Ga ta nan, ga ta nanku.
Wata rana Kurege ya je gidan Kura ya ce su tafi farautar kayan dadi Jeji.
Kura ta amince. Suka shirya suka kama hanyar daji. Da suka isa bakin rafi sai Kura ta ce, to su rabu a nan. Ta ce tun da shi Kurege karami ne ya bi cikin ciyawa, ita kuma Kura da yake babba ce. za ta bi kan hanya.
Da fari Kurege ya ki yarda, amma daga baya ya hakura, ya bi cikin ciyawa yana tafiya har ya kai ga gidan zuma, ya tarar Kudan Zumar suna
ciki. Sai ya saurare su ya ji duk sanda za su fita sukan ce: "Bude bus." sai kofar gidan ta bude, su fita. Idan sun dawo sai su ce: Rufe kif." sai kuma kofar ta rufe.
Da ya gane yadda suke yi, sai ya labe har Kudan Zuma suka fita sarai. Da ya ga haka sai ya matsa kusa ya ce: "Bude bus, sai kofa ta bude. Sai Kurege ya shiga ya kwashi zuma ya sha, ya cika jakarsa da ita, ya fito, ya dubi kofa ya ce: “Rufe kif," sai kofa ta rufe, ya kama hanya ya dawo inda suka yi alkawari za su hadu da Kura.
Ita kuma Kura da ta kama hanyarta, ta rinka tafiya ba ta ga komai ba, ga shi ta fara jin yunwa. Can dai ta hango zawayi a malale a gindin bishiya, ta je ta kama shan zawo har ta koshi.
Daga nan ta ɗebi sauran zawayin nan ta zuba a Jakarta, ta kama hanyar inda suka yi alkawari za su hadu da Kurege.
Da ta iso sai ta tarar ashe Kurege ya riga ta dawowa. Kurege ya dubi Kura, ya ce: "Kura gà shi kin ciko jakarki da kayan dadi, sai ki dan debo mini abin da kika samo,"
shima zai debo mata, ità ma ta đebo masa nata, amma idan na Kurege yaji ba dadi, zai biya ta nata.
Kurege ya yarda. Da Kura ta bude jaka sai Kurege ya fara jin warin kashi, ya dubi Kura ya ce mata ya fasa shan abin da ta zo da shi.
Da ta ji haka, sai ta ce to shi ke nan, amma ya dan ba ta nasa. Kurege ya bude jakarsa ya deba mata, ya ba ta.
Da ta ji zaƙi sai ta jefar da jakarta ta kuma ce sai Kurege ya nuna mata inda ya samo wannan zumar.
Kurege ya ce to su tafi ya nuna mata. Suka kama hanya, har suka je gidan Zuma, ya gaya mata yadda za ta bude kofar gidan Zuma.
Nan take Kura ta je ta bude gidan zuma, ta fara shan zuma har ta koshi. ta cika jakarta. Amma kuma sai ta manta yadda za ta bude ta fita, sai ta rinka cewa: "Rufe kif." Ta dai kasa fita har Kudan Zuma suka dawo daga cin furanni, suka fada wa Kura da harbi, duk jikinta ya kumbura.
Kurege ya gudu ya bar ta, daga baya ta koma gida duk fuskarta a kumbure. A gida aka tambaye ta me ya same ta, sai ta ce: "Ai na yi yaki ne da wasu namun daji, amma duk na kashe su sai dai jikina ya kumbura.
Da ta je gidan Kurege sai ya buya, ya ce: "A gaya mata ba na gida. Kura ta ce: "Idan ya dawo a gaya masa in bakinsa ya yi masa kaikayi, to ya daka da dutse kafin mu hadu," sai ta yi tafiyarta.
Da ba don Gizo ba da na yi muku karya.
Kurunkus.
Mun ciro wannan Labarin daga littafin Taskar Tatsuniyoyi na Dakta Bukar Usman
Wane Darasi Labarin yake karantawarwa...?
Mu tattauna.