Miliyoyin 'yan Najeriya ka iya fuskantar ƙarin kudin lantarki nan gaba

top-news

Al'ummar Najeriya za su fuskanci karin kudin lantarki muddin gwamnati ta ci gaba a kan shirinta na janye tallafi da kashi 15 cikin 100.

Yin hakan zai kara jefa al'ummar kasar cikin mawuyacin yanayi bisa la'akari da hakin da ake ciki na matsin tattalin arziki.

A ranar Talata ne mai magana da yawun shugaban kasar Bayo Onanuga ya sanar da shirin gwamnatin, yana mai cewa za a yi hakan ne domin a rage kashe kudaden gwamnati.

Idan aka dauki wannan mataki za a rage kashe kudaden gwamnati da kusan dala biliyan biyu da miliyan dari shida.

Ba dai a bayyana lokacin da gwamnati za ta janye tallafin kashi 15 cikin 100 ba.

Ko a yanzu ma ba kowa ba ne yake iya sayen wutar saboda yadda ta yi tsada duk da cewa farashin ya banbanta daga gari zuwa gari da kuma atsakanin unguwanni.

Cire wannan tallafi na nufin wuta za ta koma hannun 'yan kasuwa kacokan. To sai dai har kawo yanzu kusan fiye da kaso 70 na 'yan Najeriya ba su da mitar da ake sanyawa kudi.

A kwanakin baya ne dai asusun lamuni na duniya ya shawarci Najeriya da ta cire tallafin mai kacokan da kuma tallafin da take bai wa 'yan kasar a wutar lantarki.

Daga BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *