A karo Na Biyu Kungiyar NIA Ta shirya Taron Buda Baki (Iftar) a Katsina
- Katsina City News
- 30 Mar, 2024
- 687
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Kungiyar ta Nigerian Institute of Architect NIA a Reshen jihar Katsina a karo na biyu ta kuma shirya wa 'Ya'yan Kungiyar na jihar Katsina Taron Buda baki da sada zumunci, gami da karfafawa akan Kwarewa ta baiwar zane-zane da Allah yayi masu.
Kungiyar ta NIA a karkashin jagorancin shugaban ta na jihar Katsina Architect Kamaluddin Dahiru FNIA, RARCON, RTC ta shirya taron a Dakin Cin Abinci na Katsina Motel dake GRA cikin garin Katsina.
Taron karo na biyu ya samu halartar Kwarari kuma shaharrun Masu Zane na ciki da wajen jihar Katsina, Irin su jihar Kano da sauransu. An gabatar da jawabai na karfafawa juna da bada kwarin gwiwa a kan baiwar zane-zane da cigaba da ke cikin ilimin kansa. Wadanda suka gabatar da jawabai a wajen taron akwai Architect Audi daga Kano, Architect Mustapha Maikudi Kankiya da sauransu.
Bayan jawabai bisa Al'adar Taron an raba Al'quranai ga Membobin Kungiyar domin kara kyautata Ibada a cikin watan Ramadana.
Taron shan ruwan (Iftar) karo na biyu a cikin Wannan wata na Ramadan da aka gudanar a ranar Asabar 29 Maris 2024, da yayi daidai da 20 ga Ramadan ya samu halartar Mataimakin Kungiyar, Sakataren ta da Membobin gudanarwa.