ZAMFARA NA NEMAN GWAMNATIN TARAYYA TA KAMMALA MADATSUN RUWA DAKE JAHAR.

top-news

@ Katsina Times 

Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ƙara ƙaimi wajen ɗaukar nauyi tare da kammala ayyukan madatsun ruwa da ake yi a jihar.

Gwamnan ya yi kira a ranar Talata yayin ziyarar aiki da ya kai wa Ministan Albarkatun Ruwa da Tsaftar Muhalli, Injiniya Farfesa Joseph Terlumun Utsav.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce a yayin ziyarar, an tattauna muhimman batutuwa da suka shafi ayyukan ruwa a Zamfara.

A cewar sa, Gwamna Lawal ya bayyana muhimmancin madatsun ruwa wajen samar da ruwa mai ɗorewa ga ƙaruwar al’ummar jihar da kuma yadda za su bunƙasa noma da tattalin arziki baki ɗaya.

Gwamnan ya jaddada buƙatar Gwamnatin Tarayya ta ware isassun kuɗaɗe domin kammala waɗannan ayyuka, duba da irin rawar da suke takawa wajen magance matsalar ƙarancin ruwan sha a jihar da kuma bunƙasa zamantakewa da tattalin arziki.

Bugu da ƙari, Gwamna Lawal ya yi kira da a kammala tare da yin amfani da aikin madatsun ruwa a jihar domin bunƙasa noman noman rani.

A nasa jawabin, Ministan ya yi wa Gwamna Lawal alƙawarin cewa nan ba da jimawa ba za a tura tawagar ƙwararru daga ma’aikatarsa zuwa Zamfara domin tantance yanayin ruwa tare da ba da shawarar aiwatar da ayyukan da ake buƙata gaba ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *