MATSALAR TSARO; GWAMNAN ZAMFARA YA GANA DA SHUGABAN KASA.
- Katsina City News
- 27 Mar, 2024
- 377
@ Katsina Times
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya gana da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu domin tattaunawa kan yadda ake samun ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga da matsalolin tsaro a jihar.
An gudanar da ganawar ne a ranar Talata cikin sirri a ofishin shugaban ƙasa da ke fadar Aso Rock Villa, Abuja.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa Gwamnan ya yi wa Shugaba Tinubu bayani kan ƙaruwar matsalar tsaro a Zamfara, musamman yadda ake ci gaba da kai hare-hare a wasu yankuna.
A cewar sanarwar, shugaba Tinubu da Gwamnan sun tattauna dabaru da matakai daban-daban na shawo kan matsalar tsaro da suka haɗa da ƙara yawan jami'an tsaro, tattara bayanan sirri da kuma shirye-shiryen haɗa kai da al’umma.
Ganawar ya kuma bayyana buƙatar magance matsalolin da suka addabi jihar, kamar talauci da rashin aikin yi, waɗanda suke zama silar yawaitar aikata miyagun laifuka a jihar.
Wani ɓangare na sanarwar ta ce: "A yau ne Gwamna Dauda Lawal ya gana da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban ƙasa, inda suka tattauna muhimman batutuwan da suka shafi matsalar tsaro a Jihar Zamfara".
“A yayin ganawar sirrin, Gwamna Lawal ya sanar da shugaban ƙasa cewa, a cikin shekaru 13 da suka gabata, jihar Zamfara ta zama cibiyar ’yan bindiga a Arewa maso Yammacin Nijeriya."
“Gwamnan ya roƙi shugaba Tinubu da ya shiga tsakani wajen kawo isassun sojoji, makamai, da kuma kayan aiki, domin ba su isa ba a Zamfara. Ya kuma buƙaci isassun tallafi ta sama don taimaka wa sojojin ƙasa," in ji sanarwar.
Ta ce, “Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bai wa gwamnan tabbacin ba da duk wani muhimmin tallafi da dabaru ga jami’an tsaro domin tabbatar da maido da zaman lafiya a Zamfara."
Sanarwar ta ce, “Bugu da ƙari, shugaban ƙasar ya sake jaddada matsayin gwamnatin sa na ƙin yin sulhu da ’yan bindiga da kuma biyan kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane, matakin da ya yi imanin zai ƙara musu ƙwarin gwiwa ne kawai.”