ƳAN BINDIGA SUN KAI HARI ƘAUYEN SHEKEWA TA BATSARI
- Katsina City News
- 20 Mar, 2024
- 729
Misbahu Ahmad @ Katsina Times
Ƴan bindiga sun kai hari ƙauyen Shekewa dake cikin yankin ƙaramar hukumar Batsari ta jahar Katsina.
Ɓarayin sun afka ma mazauna ƙauyen mai suna Shekewa, ranar talata 19-03-2024, inda suka kwashe kimanin awonni 12 suna tafka ta'asarsu, tun shida na yamma har shida na safe (06:00pm-06:00am).
A tattaunawarmu da wani mazaunin garin, ya bayyana mana cewa "ɓarayin su kashe mutane biyar, sun raunata wasu, kuma sun cinna ma wasu gidaje wuta. Sannan suna yi masu izgilanci suna cewa wai su suke gayyato jami'an tsaro suna kawo masu hari. Sun kashe dare suna kwasar kayan mutane kamar katifu, hatsi da sauransu, suna kaiwa maɓoyarsu"
Wata majiya ta bayyana cewa dabar Ɗangote ne suka kai harin mai kama da na ramuwar gayya saboda a cikin makon nan jami'an tsaron soja sun kai masu hari kuma sunyi nasara sosai, wataƙila dalilinsu kenan na maida martani ga al'ummar wannan ƙauye, saboda azatonsu su ke gayyato jami'an tsaro suna kai masu hari.
Dama wannan ƙauye ya sha fama da hare-haren ƴan bindiga domin a nan ne 'yan bindiga suka taɓa kai wani mummunan hari har suka ƙona motocin jami'an tsaron ƴansanda biyu kuma suka kashe jami'ai biyu a shekarun baya.
Bamu samu jin ta bakin jami an tsaro ba .