Danmajalisar Tarayya a Katsina ya raba Buhunnan Hatsi da na Shinkafa 2000 a karamar hukumar sa
- Katsina City News
- 20 Mar, 2024
- 611
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Danmajalisar Wakilan Nijeriya daga Karamar hukumar Katsina Alhaji Sani Aliyu Danlami (Mai Raba Alheri) ya raba Buhunnan Shinkafa 2000 da na Gero da Masara ga Al'ummar Karamar hukumar don rage radadin halin rayuwa a cikin Azumin Ramadan.
Alhaji Sani Aliyu Danlami da yake bayyana Dalilin Wannan Yunkuri yace, "Yunkurin Maigirma Gwamnan jihar Katsina na cika jihar sa da Abinci yasa duk wani mai iko, kuma mai kishi da tausayin Al'ummar sa dole yabi sahun Dakta Dikko Umar Radda". Yace wannan yasa muma mukaga ya dace mu zo mu kara daga kokarin da Gwamna yake.
Kamar yanda Danlami ya bayyana cewa, Buhunnan Abinci, Gero, Masara, da Shinkafa mai nauyin Kilogiram 25 an kasashi bangarori uku, na farko Talakawa Masu rauni (Masu bukata ta Musamman) Mutum 1000 zasu amfana, sai Kungiyoyi guda 500, sai kuma ɓangarori Jam'iyyar APC a matakin karamar hukumar Katsina suma zasu amfana da sauran kason.
Tun da farko wakilan Jam'iyyar APC a matakin jihar Katsina Alhaji Bala Abu Musawa, ya yaba wa Hon. Danlami akan irin kokarin da yake na kyautatawa al'umma, sana yayi kira ga sauran 'yan Siyasa da suyi koyi da irin yanda Alhaji Sani Danlami yake na ganin ya fita hakkin al'umma da suka zabe shi.
Babban bako mai jawabi a wajen taron gwamnan jihar Katsina malam Dikko Umar Radda ya bayyana yaba da kuma bayyana cewa irin wannan rabo da ake na ciyar da al'umma yanzu ma aka fara, kuma zaici gaba a dukkanin kananan hukumomin jahar Katsina." Gwamnan yace a kudirin da gwamnatin sa take da shi, ba nufin su, raba abinci ba kawai nufinsu shine samar da Ayyukan yi da sana'ar da su kansu wadanda suke amsa suma su raba watarana idan suka samu jarin da zasu dogara da kansu.
Manyan baki, 'yan Siyasa na ƙaramar hukumar Katsina sun samu halartar sheda rabon tallafin da malaman jihar Katsina. Taron ya gudana a tsohon gidan Gwamnatin jihar Katsina a farfajiya hukumar bada agajin gaggawa ta SEMA.