An kuɓutar da ɗaliban Jami'ar Tarayya ta Gusau guda biyar
- Katsina City News
- 17 Mar, 2024
- 364
An kuɓutar da ɗaliban Jami'ar Tarayya ta Gusau da ke jihar Zamfara guda biyar cikin ɗalibai da aka sace.
Wata ƴar uwar ɗaya cikin ɗaliban da aka sace wadda ta buƙaci a sakaya sunanta, ta faɗa wa BBC cewa a ranar Asabar ne ƴar uwarta da aka sace ta kira ta a waya take faɗa mata cewa sun samu kuɓuta suna Abuja.
"Ta faɗa mana cewa an ɗauko su ne daga dajin birnin Gwari inda aka kawo su bakin titi aka damƙa su ga sojoji. Ta ce su tara aka dawo da su, inda sauran na can a hannun ƴan bindiga," in ji ƴar uwar ɗalibar.
Ta ce suna farin ciki da dawowar ƴar uwarsu da kuma saura da aka saki bayan shafe sama da watanni biyar a hannun ƴan bindiga.
Har ila yau, ƴar uwar ɗaya daga cikin ɗaliban da suka kuɓuta, ta ce ƴar uwar tasu a faɗa musu cewa ƴan bindigar sun lakaɗa musu duka, tare da ba su masara kawai.
Ta ce akwai ƴan mata guda uku da suka yi yunkurin tserewa har sau biyu ana kama su, inda ɗaya daga cikinsu ma ba ta da lafiya a yanzu.
"Ta ce suna ɗa yawa sun kai su kusan 40, amma a hankali wasu na ta guduwa. Ba su sani ba waɗanda suka gudu sun samu komawa gida ko kuma an kashe su a hanya ba," kamar yadda ƴar uwar ɗalibai ta shaida wa BBC.
Ta ce cikin mutum tara da aka saki yanzu sun kunshi ɗalibai mata biyar na jami'ar, inda saura huɗu kuma suka kasance leburori.
A watan Satumban bara ne yan bindiga suka yi won gaba da ɗalibai da dama a ɗakunan kwanansu da ke wajen Jami'ar ta Gusau a jihar Zamfara.