Sanata Abdul'aziz Yar'adua Na Cigaba Mika Tallafi Ga Al’ummar Mazabar Sa
- Katsina City News
- 17 Mar, 2024
- 443
Jiya ne asabar 16/03/2024 Sanata mai wakiltar shiyar Katsina ta tsakiya Sanata Abdul'aziz Musa Yar'adua, Mutawallen Katsina ya ziyarci Karamar Hukumar Danmusa don kaddamar masu da shirin sa na rabama gajiyayyu da masu bukata ta musamman tallafin da ya fara badawa inda kowace mazaba mutum dari ne zasu amfana da tallafin.
Yayin taron shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar ya bayyana godiyar sa da nuna jin dadin sa bisa irin kulawar da Sanatan kema wannan karamar hukumar ta Danmusa wanda ko sati biyu ba'ayi ba Sanata ya shiga lungunan da suke da matsalar tsaro don ganin halin da al'ummar shi suke tare da jajanta masu yakuma ziyarci dukkan sansanin da jami’an tsaron mu suke inji shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar ya koma yi fatan alheri ga Sanatan.
Shima anashi jawabin Sanatan ya bayyana godiyar sa ga Allah da yabashi ikon halartar wajen don mika tallafin ga al'ummar ya kuma bayyana cewa zai zagaye kowace karamar hukuma da kansa don gabatar da tallafin ga al'ummar shi da kansa.
Yayi kira ga al'umma da su cigaba da yima masu addu'ar samun nasara yayi gudanar da jagorancin nasu musamman mai girma gwamna bisa namijin kokarin da yake wajen ganin ankawo karshen matsalar tsaron data addabi al’umma.
Shima wakilin shugaban karamar hukumar kuma shugaban kansiloli na karamar hukumar ya bayyana godiyar su amadadin dukkan al'ummar karamar hukumar ta Danmusa.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Alhaji Abu Bala Saulawa, Hon Halilu Manjo Karofi, Hon Tanimu Sada, Hon Jabiru Yau-Yau State Exco na shiyar Katsina dadai sauran su.