"Gaskiya da Rikon Amana sune Jigon Gwamnatin Mu, Ku ma ku bada Fifiko akan Haka" -Daudaa ga Majalisar Zartaswar Zamfara
- Katsina City News
- 11 Mar, 2024
- 567
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada buƙatar yin riƙo da gaskiya da riƙon amana a harkokin gudanar da mulki, inda ya buƙaci ɗaukacin ’yan majalisar zartarwar jihar da su ba da fifiko wajen gudanar da ayyukansu a kan haka.
A ranar Litinin ɗin nan ne Gwamnan ya jagoranci zaman majalisar zartarwa ta Jihar, wanda aka gudanar a zauren majalisar da ke gidan gwamnati a Gusau.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta bayyana cewa majalisar ta tattauna batutuwa daban-daban da suka shafi ci gaban jihar da suka haɗa da samar da ababen more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi, da kuma tsaro.
A cewar sanarwar, wannan shi ne taron majalisar zartarwa karo na goma sha takwas tun bayan da aka ƙaddamar da "shirin ceto Zamfara."
Majalisar ta tattauna kan ci gaban da aka samu a fannin samar da ababen more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi, da tsaro da dai sauransu.
A wajen taron, Gwamna Lawal ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ganin jihar ta cimma manufofinta na ci gaban al'umma.
Gwamnan ya ja hankalin ’yan majalisar kan su kasance masu himma da ƙwazo wajen gudanar da ayyukansu.
Bugu da ƙari, an gabatar wa majalisar da cikakken rahoto kan halin da ake ciki na aikin gyaran sakatariyar jihar da ake yi. Rahoton ya bayar da cikakkun bayanai kan ci gaban da aka samu kawo yanzu, ciki har da kammala aikin gyare-gyare kashi na farko.