Gwamnan Kaduna ya yi alƙawarin ceto dukka ɗaliban da aka sace a Kuriga
- Katsina City News
- 08 Mar, 2024
- 393
Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya yi alkawarin ceto dukkan daliban da ‘yan bindiga suka sace a Kuriga da ke karamar hukumar Chikun a jiya Alhamis.
Gwamnan ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da ya ziyarci al’ummar yankin domin jajanta musu kan lamarin.
Sai dai ya ce ba a tantance adadin wadanda aka yi garkuwa da su ba, amma gwamnati na hada kai da mahukuntan makarantar da sauran al’umma domin samun ainihin adadin.
Gwamnan ya shaidawa al’ummar yankin cewa ya samu tabbacin goyon bayan shugaban kasa Bola Tinubu da kuma mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu domin a dawo da daliban gida lafiya.
Ya kuma buƙaci al’umma da kada su karaya, su hada kai da gwamnati wajen ganin an ceto yaran tare da karfafa tsaro a wurin.
Gwamna Sani ya kuma yi kira ga iyayen yaran da aka sace da su yi hakuri, yana mai tabbatar da cewa gwamnati ba za ta kyale su ba.
Gwamnan ya ce lamarin ya kishi zafi a rai, don haka ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an dawo da daliban firamaren da sakandaren gaban iyayensu.