Barawo Ya Haura Katangar Gidan Gwamnan Katsina, Ya Shiga Dakin Matarsa?
- Katsina City News
- 07 Mar, 2024
- 2927
Muazu Hassan @Katsina Times
Ana wani zargi mai karfin gaske cewa wani barawo ya haura katangar gidan gwamnatin Katsina ya keta duk wani shingen tsaro ya shiga gidan da Gwamna Malam Dikko Umar Radda yake zaune da iyalansa.
Ana zargin barawon ya shiga har dakuna ya yi buruntu, sai dai babu wani tabbacin me ya yi nasarar dauka, ko kuma shiga kawai ya yi ya fita?
Lokacin da muka tuntubi mai magana da yawun Gwamnan Katsina, Ibrahim Kaulah Muhammad a kan gaskiyar labarin, cewa ya yi labarin jita-jita ne, babu wani kamshin gaskiya a tare da shi.
Ya ce jita-jitar ta fara ne a ranar da Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umar Radda ya kai ziyarar jaje ga mutanen garin Wurma da ke karamar hukumar Kurfi a kan ta’addacin da barayin daji suka yi masu. Kaulah ya ce a ranar aka fara yada wannan jita-jitar.
Amma binciken da jaridun Katsina Times suka yi daga majiyoyi daban-daban a gidan na gwamnatin Katsina, sun tabbatar mana cewa lallai a ranar Lahadi 3 ga watan 3 da misalin karfe 1 na dare, jami an tsaron gidan sun lura da akwai wani bakon da ba a so a cikin gidan, kuma suka fara daukar matakin yi masa kofar raggo don su kama shi.
Majiyarmu ta ce, nan da nan jami’an tsaron suka dau matakin yadda za su kama wanda ya shigo, har bindiga an harba, kamar yadda majiyar ta tsegunta mana.
Majiyarmu ta ce kyamarar tsaro da ke daukar hoton gidan ta dauko wannan mutumin wanda ya yi shigar da ko an dauki hotonsa ba za a gane shi ba.
Majiyarmu ta ce, kyamarar ta tsaro ta dauko hotonsa yadda ya hauro ta katangar baya har ya shiga gidan, kuma ta dauko hoton yadda ya fita ta kantangar bayan gidan, bayan ya lura an farga yana ciki ana neman kama shi.
Majiyarmu ta tabbatar mana da cewa a lokacin da abin ya faru, Gwamnan na Katsina da mai dakinsa suna cikin gidan.
Majiyar tamu ta ce Gwamnan na Katsina ya umurci rundunar ’yan sanda ta binciki lamarin, binciken da ake ci gaba da yi a daidai lokacin da muka rubuta wannan rahoton.
Mun tuntubi mai magana da yawun rundunar ’yan sanda na jihar Katsina, ya dauki wayarmu, amma ya ce zai sake kira daga baya, bai sake kira ba. Mun aika masa da sakon kar-ta-kwana bai ba mu amsa ba har ya zuwa lokacin da muke hada wannan rahoton.
Bincikenmu ya gano wannan shi ne karo na farko da aka taba haura kantangar gidan gwamnatin jihar Katsina aka yi kokarin yin sata tun da aka gina shi aka tare a shekarar 2017.
A lokacin Gwamna Aminu Bello Masari, an sami zargin shiga ofis dinsa, inda aka ajiye wasu kayan kulumboto, ana zargin har da sata, amma kyamarar tsaro ta dauki hoton komai, kamar yadda jaridar Taskar Labarai ta ba da labarin a wancan lokacin.
Kuma a lokacin har wanda ake zargi sai da jaridar ta samu sunansa, kuma ta yi magana da shi, inda ya karyata. Ya ce bidiyon wanda aka dauka bai yi kama da shi ba, amma ya tabbatar da faruwar lamarin a wancan lokacin.
ME YA KAWO AKA KETA TSARON GIDAN?
Jaridun Katsina Times sun zanta da wasu jami’an tsaron da ke ba gidan gwamnatin kariya bisa amana, sun fada mana cewa suna aikinsu tsakani da Allah, kuma suna jinjina wa Gwamnan Katsina Malam Dikko Radda bisa da yake kula da bukatunsu na yau da kullum.
Suka ce a duk gwamnatocin da suka wuce, saboda an san aikinsu dare da rana ne gidan gwamnati ke ba su abinci sau uku a rana. Suka ce sabbin masu kula da gidan yanzu sun dakatar da wannan.
Sun kara da cewa, yanzu su ke daukar nauyin ciyar da kansu da kansu. Suka ce wasu haka suke zama kwana da kwanaki daga ruwa sai burodi.
Sun bayyana mana cewa, wasu da suka rika addu’ar Allah ya sanya a kai su aiki gidan gwamnati, yanzu suna bayar da sadaka Allah ya sanya a dauke su.
Jami’an da suka bukaci mu sakaya sunansu, sun tabbatar mana da cewa wasu haka za ka gan su rataye da bindiga sun je neman abincin sayarwa na kan titi irin wanda ake kira “gafara mahaukaci.”
Wadanda muka zanta da su sun ce, wasu jami an tsaron da ka gani a gidan gwamnatin Katsina a yanzu a cikinsu, wasunsu ko dai suna jin yunwa ko sunna zullumin ina zai samu na ci in anjima.
Mun yi kokarin tabbatar da wadannan zarge-zargen na hadin gwiwar jami’an tsaron da ke aiki a gidan gwamnatin, amma lamarin ya ci tura.
Mun yi kokarin jin ta bakin mai magana da yawun Gwamnan Katsina, amma ba mu samu nasara ba. Mun kuma kira wayar shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Katsina don jin ta bakinsa bai dauki wayarmu ba.
Mun bi wata hanyar don jin ta bakinsa duk ba mu yi nasara ba, mun aika da sakon rubutu ba amsa, mun saurara awa 48 don amsa babu.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.taskarlabarai.com
07043777779 08057777762
Email; newsthelinks@gmail.com