ƳAN BINDIGA SUN KAI HARI YANKIN BATSARI
- Katsina City News
- 28 Feb, 2024
- 678
Misbahu Ahmad @ Katsina Times
Ƴan bindiga sun kai hari ƙauyen salihawarɗan'alhaji dake cikin yankin ƙaramar hukumar Batsari ta jahar katsina.
Lamarin ya faru da misalin 08:30pm na daren litanin 26-02-2024, inda ƴan bindiga masu satar dabbobi da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa, suka afka ma ƙauyen dake matsaɓar Ɗan'alhaji/ƴangayya. Sun kunna ma rumfuna da zabaro kara wuta, kamar yadda wani mazaunin ƙauyen ya shaida ma wakilinmu, sun yi garkuwa da mutane goma, galibinsu mata ne.
Wata majiya ta bayyana cewa, an sanar da jami'an tsaro lokacin da abun ke faruwa amma ba'a kai masu ɗauki ba.
Hare-haren ƴan bindiga ba sabon abu ba ne a yankin Batsari, domin ko a ranar lahadi 25-02-2024 wani ayarin na ƴan bindiga sunkai hari ƙauyen Ajasu, inda suka sace mutane bakwai mata shida namiji ɗaya, amma wata majiya ta shaida mamu matan sun dawo saura namijin ke hannunsu.