"Muna neman Addu'a, Shawara da Haɗin kan dukkanin Malamai." Kwamandan Hizbah a Katsina
- Katsina City News
- 08 Feb, 2024
- 650
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Dakta Aminu Usman (Abu Ammar) Babban Kwamandan Hukumar Hizbah na jihar Katsina, ya nemi hadin kan Manyan Malaman jihar Katsina da sauran Al'umma akan gudanar da Ayyukan na Hizbah.
A ranar Alhamis 8 ga watan Fabrairu, hukumar ta Hizbah bisa jagorancin Shugaban nata Dakta Aminu Usman ya shirya wani rangadi na ziyarar Manyan Malamai, masu rike da sarautun gargajiya da bangarorin jami'an tsaro don neman hadin kai, shawara, da kuma Addu'a gare su akan gudanar da Ayyukan na Hizbah.
Aminu Usman ya bayyana cewa "Mun fito ne domin Neman Addu'a, Tabarruki, da Shawarwarin ku Malaman Addini da Jami'an tsaro domin a gudu tare a tsira tare." Yace bisa umurnin maigirma Gwamnan jihar Katsina malam Dikko Umar Radda, ya kuma samar da wannan hukuma ne ba don komai ba sai don ganin yanda gurbacewar tarbiyya tayi yawa a cikin al'umma". Ya bayyana A yayin gudanar da ziyarar ga malamai.
Ziyarar da ta shafi Dukkanin malaman Addinin Musulunci na bangarorin Izala, Dariƙa, Shi'a da Qur'aniyyun, Dakta yana bayyana manufofin ziyarar da kuma abinda hukumar ke nema ga malaman.
Dakta Abu Ammar ya bayyana cewa Hizbah tana da bangarori daban-daban, domin tabbatar da gyara a cikin al'umma, yace daga ciki akwai sasanci musamman na gyaran Aure, daidaita lamurra da ilmantarwa akan zaman Aure, don rage mace-macen Aure. Aurar da Zawarawa da sauransu.
Ziyarar ta Hukumar Hizbah ta ziyarci, Babban Malamin Dariqa Sheikh Iyal Gafai, Sheikh Liman Abba, Sheikh Muhammad Surajo, Malam Kabir Makurda Kofar Sauri, Babban Limamin Katsina, Zawiyyar Sharif Abba Abu Rafindadi. Da bangaren masu sarautar gargajiya a ofishin Magajin garin katsina, da Jami'an tsaron 'Yansanda Ofishin Kwamandan yanki (Area Commander) da DPO na karamar hukumar Katsina.
Dukkaninsu sun yaba sunyi Addu'a da fatan Alheri gami da shawarwari da kuma bada hadin kai a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
A cikin tawagar akwai Kungiyoyin Munazzamatu Fityanul'islami, Nasrul'islami, Kungiyar Agaji da sauransu.
Sabuwar hukumar ta Hizbah a karkashin jagoranci Babban Kwamandan nata Dakta Aminu Usman zataci gaba da ziyarar inda ake sa ran zata ziyarci dukkanin manyan zawiyoyi, limamai da bangarorin tsaro na jihar Katsina a kananan hukumomi 34.