Mummunar Zanga-zanga akan Matsayin Rayuwa ta barke a jihar Arewa
- Katsina City News
- 05 Feb, 2024
- 602
Mummunar zanga-zanga ta barke a jihar Arewa kan yanayin halin kunci da ake ciki, bayanai sun fito
Mazauna birnin Minna da ke jihar Neja sun fito zanga-zangar nuna rashin jin dadi kan tsadar rayuwa a kasar. Legit ya wallafa.
Mutanen sun fito zanga-zangar ce a yau Litinin 5 ga watan Faburairu inda suka cika titunan birnin, cewar Channels TV.
Masu zanga-zangar da suka hada da mata da matasa sun cika titunan birnin tare da rera wakoki yayin da jami’an tsaro ke kallonsu.
Matasan suka ce tsadar rayuwa a kasar musamman kayayyakin abinci da kuma rashin yin wani abu kan lamarin shi ne dalilin zanga-zangar.
Suka ce sun dauki matakin yin zanga-zangar ce don gwamnati ta ji kukansu tare da daukar matakin dakile matsalar.
Mataimakin gwamna jihar, Yakubu Garba yayin jawabi ga masu zanga-zangar ya ce suna sane da halin da ake ciki, cewar Daily Post.
Ya ce duk wata wahala da jama'ar kasar ke fama da shi sun sani inda ya ce su na duk abin da ya dace don dakile matsalar.
Har ila yau, ya ce akwai wasu matakai da ake da su a kasa don rage hauhawan farashin kayayyaki dalilin cire tallafin man fetur.