An dakatar da Janye Aikin Fadada Filin Jiragen Sama na Katsina

top-news

Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times

Ministan Sifirin Jiragen Sama na Najeriya Mr. Festus Keyamo ya janye kudirin sa na karkatar da fadada Filin Jiragen Sama na Malam Umaru Musa Yar'adua da ake cikin yi a halin yanzu.

Hakan ya biyo bayan kiraye-kiraye da kungiyoyi Matasa masu raji da kishin jihar Katsina, gami da Kungiyar Dattawan jihar Katsina suka yi, da ya kai ga kunnen 'yan Majalisar Dokokin Tarayyar Nijeriya, a jihar Katsina da basuyi kasa a gwiwa ba suka garzaya har ofishin Ministan don nuna masu rashin amincewar su.

A zantawar da bbc hausa tayi da Danmajalisar Tarayya daga jihar Katsina Hon. Sada Soli Jibiya ya tabbatar da cewa ministan Sifirin Jiragen Sama Mr Festus Keyamo ya janye kudirin nasa, yace kamfanin da ke aikin kwangilar ne ya bada shawara da juya aikin zuwa jihar Legas yanzu kuma babu wannan maganar.

Sada Soli ya bayyana cewa, ko shakka babu aikin fadada filin Jirgin zaici gaba kamar yanda ministan ya tabbatar, kuma samar da filin jirgin zai kara fadada cigaba da samar da aikin yi a jihar Katsina.

Aikin fadada filin Jirgin da tsohon ministan Sifiri na Gwamnatin Buhari ya samar tun a shekarar 2022 zai lashe makuden miliyoyin Nairori, wanda a cikin ne za a samar da sashin gyara da kera Motocin kashe gobara ta jiragen sama, da filin sauka da tashin manyan jirage wanda ake saran zai zama irinsa na farko a yammacin Afirka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Tasiu Abubakar

Allah mum GODE Maka da mukasamu irin waddan datawa da matsala MASU kishin kasa da jahar Katsina, Muna Ron Allaah ya I gaba da bamu basará a Koda yaushe alfarmar fiyayyen halitta SAWW