Rundunar Sojoji a jihar Katsina sun ceto Mutum 35 da aka yi garkuwa dasu a Batsari
- Katsina City News
- 29 Jan, 2024
- 560
Rundunar Sojoji a jihar Katsina sun ceto Mutum 35 da aka yi garkuwa dasu a Batsari
Muhammad Aminu Kabir
Rundunar sojin Najeriya a jihar Katsina tayi nasarar ceto mutane 35 daga hannun ƴan bindiga waɗanda aka sace garin Tashar Nagulle da ke ƙaramar hukumar Batsari a jihar Katsina kimanin Mako guda da ya gabata.
Bayanai sun bayyana cewa Sojojin sun fatattaki maboyar ƴan bindigar ne bayan samun bayanan sirri suka kai farmaki a maboyar ƴan bindigar tare da kubutar mutanen da suke tsare dasu.
Daga cikin mutanen da sojojin suka kubutar aƙwai matan aure da maza da ƙananan yara wanda suka bayyana irin halin ƙuncin da suka samu kansu a hannun ƴan ta'addar, sun bayyana kalar abincin da ɓarayin ke basu, Dawa ce kaɗai abincin da ake basu a kowace rana a cewar su.
A makon da ya gabata ne, tun a ranar Lahadi 21 ga watan Janairu 2024. ƴan bindigar suka kai wani hari a kauyen Tashar Nagulle inda suka yi garkuwa da mutum 35 zuwa daji kuma suka buƙaci a basu Naira miliyan 60 a matsayin kuɗin fansa.
Shugaban ƙaramar hukumar Batsari Alhaji Yusuf Mamman Ifo, shi ne ya tabbatar da kubutar da mutanen 35 da sojojin suka yi inda ya ce ana duba lafiyarsu kafin daga bisani a maida su ga iyalansu.
Ya zuwa yanzu babu wani ƙarin haske daga rundunar Sojojin akan kubutar waɗannan bayin Allah da irin artabun da akayi ko an samu nasarar halaka ɓarayin ko an kama wasu.