Dan Majalisar Wakilan Nijeriya a jihar Katsina ya Ziyarci Gundumar Daudawa a ci-gaba da Yakin neman zaben cike giɓi
- Katsina City News
- 26 Jan, 2024
- 706
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Tawagar Yakin neman Zaben Danmajalisar Tarayya mai Wakiltar Kananan Hukumomin Kankara, Faskari da Sabuwa Hon. Muhammad Jamilu Lion ta ziyarci Gundumar Daudawa a karamar hukumar Faskari.
Dimbin Al'umma magoya bayan Jam'iyyar PDP da lungu da sako na Mazabun ne sukayi cincirindon don tarbar Danmajalisar, wanda ya ziyarci akwatinan zaɓen don kara neman goyon bayan al'ummar sa a yankunan da za a canza zabe, inda al'umar yankin suka sanyawa gangamin suna "Fadi da Cikawa"
Dan takarar da tawagar sa sun zagaya mazaɓu guda hudu dake Daudawa, wanda za'a sake zabe a wadannan yankuna da suka hada da Daudawa, Tudun Malamai, Kwankiro, Kanon haki, Duka a karamar hukumar Faskari.
Tawagar yakin neman zaben ta Danmajalisar Tarayya Muhammad Lion ta samu rakiyar tsohon shugaban Jam'iyyar PDP na jihar Katsina Alhaji Kabir Maiwada Daudawa da shugaban riko na jam'iyyar PDP a karamar hukumar Faskari Hon. Khalid Adamu Bilbis da sauran masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a karamar hukumar Faskari.
Al'umar mazabun sun cika Unguwanni don yima Danmajalisar Kyakkyawar Tarba da fatan Alheri a zaben da za a gudanar da cike gibi wato (By-election)