Hadin gwiwar Jami'an Tsaro sun yi Taho mu gama, da Barayin Daji a Dandume, ...sun kashe wasu kuma sun gudu
- Katsina City News
- 26 Jan, 2024
- 663
Daga Shamsu Wapa Dandume
Daren jiya Alhamis Da Misalin karfe takwas wasu gungun Yan ta'adda, masu garkuwa da mutane sunyi yunkuri shigowa cikin garin Dandume Jihar Katsina domin aikata ta'addanci, Cikin ikon Allah sai aka sami labari cikin gaggawa, nan da nan jami'an tsaron mu na Soja, Yan Sanda, da kuma Jami'an CWC suka hada Joint Operation inda aka ritsasu a bayan gari.
Kamar Yadda Majiyar Karaduwa Post, Ta Shaida Mana, Bayan musayar wuta da jami'am tsaro da kuma su Yan'tadda na kusan Awa daya, anyi nasarar halaka mutum daya daga cikinsu, inda sauran abokan ta'addancin nasa suka juya da munanan raunuka a jikin su.
Bayan Bata Kashin Da Akayi da barayin dajin a shekaran jiya, Nan Ma Dole suka ranta na kare.