Ana ƙoƙarin Karkatar da Aikin Fadada Filin Jiragen Sama na jihar Katsina
- Katsina City News
- 22 Jan, 2024
- 647
Zaharddeen Ishaq Abubakar
Wasu takardu da suka bayyana na nuna da yanda ake kokarin karkatar da Fadada Filin Jiragen Sama na Malam Umaru Musa Yar'adua zuwa kudancin Kasarnan, Kasantuwar haka yasa gamayyar kungiyoyin Fararen Hula a jihar Katsina, da suka hada da Kungiyar Muryar Talaka, da Kungiyar wayar da kan 'yan Kasa game da yaki da cin hanji da rashawa, (CPAC) da Kungiyar wayar da kan yan kasa game da zaman lafiya da tsaro (KYECOPAD) suka kira taron manema labarai don bayyanawa Al'ummar Katsina da ta Arewacin Nijeriya halin da ake ciki.
Sana kuma kungiyar tayi kira ga Shugaban Nijeriya Malam Bola Ahamed Tunubu da ya tsawatarwa Ministan sa mai kula da wannan ayyukan wato Mista Festus Keyamo ministan Sifirin Jiragen sama.
A taron na manema labarai da ya gudana a dakin taro na sakatariyar kungiyar NUJ ta jihar Katsina, an bayya cewa aikin kwangilar an bada shi ne a lokacin mulkin tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a shekarar 2022.
"Wannan aiki yana da tasiri kwarai da gaske akan ci gaban tattalin arzikin jihar Katsina da Najeriya, bakidaya. To sai dai kash, mun samu wasu takardu da ke, nuna ana neman a karkatar da wannan aiki daga jihar Katsina zuwa wata jiha a kudancin Najeriya." Inji sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa "Wannan na faruwa ne duk da matsayar shugaban kasar Nijeriya, Bola Ahmed Tunubu cewa Gwamnatin shi za ta kammala dukkanin Ayyukan da Gwamnatin baya ta fara."
"To amma wannan danyen mataki da Keyamo ke yunkurin dauka, na ya nuna ya yi hannun riga da kudurin Shugaban ƙasa."
"Ga dukkan alamu, Mista Festus Keyamo, nada wata bakar Aniya ta kokarin bata ministan da ya gada, Inda duk wani aiki da ministan da ya gada ya yi, yake bi daya bayan daya, yana ruguza su." inji sanarwar.
"Saboda haka ne, mu wadannan kungiyoyi,muke kallon wannan mataki na kokarin dakatar da wannan aiki, a matsayin zagon kasa ga al'ummar jihar Katsina, wadanda suka fito a lokacin zaben da ya gabata, suka kada ma Bola
Ahmed Tunubu kuru'u da suka taimake shi ya zama shugaban kasa, a daidai lokacin da Keyamo yake a social media yana Zage-zagenshi.
"Mu mutanen jihar Katsina, muna son filin Jirgin mu, saboda muhimmancin sa ga ci gaban mu. Sama da shekaru goma, ta wannan filin jirgin dubban maniyyatan mu ke tashi zuwa kasar Makka domin Aikin Haji. Kazalika, kwananan muke fatan za a fara daukar masu zuwa aikin Umra kai tsaye.
Baya ga aikin Ibada, akwai jiragen 'yan kasuwa masu jigilar fasinja, dake tashi da sauka a wannan filin jirgi kowace rana ta Allah.
"Kazalika, wannan ne, filin jirgin sama na kasa da kasa, dake kusa da filin jirgin saman mallam Aminu Kano, wanda kilomita 142 ne tsakanin su. Saboda haka, koda wani abu na gaggawa zai tashi, wannan filin jirgi namu zai taimaka."
"Jihar Katsina muna bukatar filin jirgin sama, kuma muna so a inganta shi, a gyara shi, ya iya gogayya da kowane irin filin jirgin sama a duniya." Inji takardar sanarwar.
A karshe Kungiyoyin sun yi kira ga Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umar Radda, 'Yan Majalisun Tarayya da Masu ruwa da tsaki a jihar akan kada su yadda aikata wannan danyen Aiki. Sana kuma sunyi kira ga dan kwangila da idan har ba zai iya ba ya zame jikinsa wani ya karba.