Hatsarin Kwale-kwale Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 8, Kimanin Wasu 100 Kuma Sun Ɓace A Kogin Neja
- Katsina City News
- 17 Jan, 2024
- 483
Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya ta sanar a jiya Talata 16/01/2023 cewa fasinjoji takwas ne aka tabbatar sun mutu, sannan kimanin wasu 100 kuma sun bace, bayan kifewar kwale-kwalen da suke ciki a arewa maso tsakiyar kasar.
Wannan dai shi ne na baya-bayan nan a jerin munanan hadurran kwale-kwale da ke kara bayyana kasawar tsarin kula da bin doka a kasar.
Ana jigilar fasinjojin ne daga gundumar Borgu ta jihar Neja zuwa wata kasuwa da ke makwabciyar jihar Kebbi a yammacin ranar Litinin, lokacin da jirgin ya kife a kogin Naija, kamar yadda kakakin hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja Ibrahim Audu ya bayyana.
"An yi wa kwale-kwalen lodi fiye da kima don haka ne iska mai karfi ta shafe su suka kife," in ji Audu.
Ya ce karfin kwale-kwalen shi ne daukar fasinjoji 100, amma an kiyasta cewa yana dauke da adadi mai yawa, baya ga buhunan hatsi, lamarin da ya sa da wuya a iya daidaita shi lokacin da ya fara nutsewa.
Mazauna ƙauyukan na taimakawa ƴan ninkaya da jami’an agajin gaggawa don nemo fasinjojin da suka ɓata, waɗanda yawancinsu mata ne, in ji Audu. To sai dai bai bayyana adadin mutanen da suka tsira ba.
Hadurran kwale-kwale ya zama ruwan dare a cikin al'ummomin yankunan karkara a faɗin Najeriya, inda mazauna yankin da ke buƙace da hanyar kai kayayyakin amfanin gonakinsu zuwa kasuwa, su kan yi cunkoso a cikin kwale-kwalen kirar gida sakamakon rashin kyawawan titunan mota.
Kawo yanzu dai babu tabbataccen adadin waɗanda suka mutu a waɗannan hadurran, ko da yake an sami aƙalla hatsari biyar da suka haɗa da fasinjoji aƙalla 100 kowanne a cikin watanni bakwai da suka gabata, yana da Matuƙar Muhimmanci hukumomi su kawo wani tsari mai Kyau da zai rage asarar rayuka da dukiyoyin Al'umma ta hanyar samar da jiragen ruwa na zamani a waɗannan yankunan.
-AP