Ɓarayin Daji Sun Ƙona Direba da Yaron sa a cikin Motar Kayan Amarya A Katsina.
- Katsina City News
- 11 Jan, 2024
- 863
Yadda ɓarayin daji suka tare motar kayan Amare tsakanin ƙaramar hukumar Jibia zuwa ƙaramar hukumar Batsari jihar Katsina.
A daren ranar Talata 08/01/2024 ne ƴan ta'addar daji dake kan hanyar Jibia zuwa Batsari suka tare wata mota ɗauke da kayan wasu Amare guda Ukku da suka haɗa da Gadaje Kujeru da Katifu guda huɗu, Inda basuyi wata wata ba suka banka masu wuta.
Ɓarayin dai sun hana Direban da yaron shi fita daga Motar Inda suka ƙone ƙurmus tare da kayan da suke ɗauke dasu.
An samu gawar Direban mai suna Babangida Garba Turaki wanda akayi mashi sutura a jiya amma shi yaron Motar Auwal Malle ba a ma Iya samun gawar shi ba domin ya ƙone ya zama toka ko Gawayi.
Wannan hanya dai dake tsakanin Jibia zuwa Batsari har yanzu tana ci gaba da zama ƙarƙashin kulawar waɗannan ɓarayin daji bin ta ya zama tashin hankali.
Wani da muka zanta dashi ya kuma tabbatar da haruwar lamarin yace Lamarin ya faru ne a wani wurin da ake cema Sola ta ɓangaren ƙaramar hukumar Jibia kafin a kawo Batsari, motar kuma ta taso ne daga cikin garin Katsina ƴar Kasuwa zata kai kayan wasu ƙauyukan dake tsakanin Jibia da Batsari.
Akwai buƙatar Gwamnati ta ƙara matsa ƙaimi akan waɗannan miyagun Mutane da basu da tausayi bare ɓarɓashin imani a zukatan su, mun sani irin waɗannan hare haren suna nuna raunin Ƴan ta'addar ne bisa matsin lambar da suke samu daga Jami'an tsaro.
Allah yajiƙan su da Rahama ya kyautata Makwanci Amin. Muhammad Aminu Kabir