RIKICIN PDP A JAHAR KATSINA;SAI KARA MUNANA YAKE
- Katsina City News
- 10 Jan, 2024
- 585
Muazu Hassan
@ Katsina Times
Jam iyyar PDP a jahar Katsina sai kara tsunduma take a cikin rikici kamar wadda cutar kanjamau da magani yaki amsa take yi .
Wannan ya jawo " yan jam iyyar sai kaura suke suna barin jam iyyar kamar farin Dango, jiga jigai a jam iyyar sai barin jam iyyar suke.misali a karamar hukumar Katsina kwamishin lafiya na jahar dakta bishir Gambo saulawa na cikin wadanda sukayi jawabi a wajen amsar wasu yan jam iyyar daga PDP zuwa APC .
A karamar hukumar Batsari Barista Ahmad Danbaba Wanda ya taba yi ma jam iyyar mai bada shawara akan harkokin Shari a.ya kuma taba zama mai ba gwamnan Katsina shawara a jam iyyar ya zama shugaban karamar hukumar ta Batsari ya fice daga jam iyyar ya koma APC.
Rikicin ba ya bayan nan da ya faru shine a watan da ya wuce masu ruwa da tsaki suka so yin taro a hotel din Makera dake Katsina karkashin jagorancin..sanata Tsauri amma wasu mutane da ake zargin tsohon Dan takarar gwamna a jam iyyar ta PDP ya tura su suka tarwatsa taron.
Binciken jaridunmu ya tabbatar sama da kananan hukumomin ashirin sunyi koke akan yan Kwamitin riko da aka Dora masu.wannan ya sanya Kwamitin riko na jaha yace duk inda ake da korafi a sake lale.
Wannan matsaya na Kwamitin riko na jaha bai yi ma bangaren tsohon Dan takarar gwamna a jam iyyar dadi ba.
Wannan ya sanya ake zargin .tsohon shugaban jam iyyar ta PDP Alhaji lawal Magaji Dan baci ya kai kara babbar kotun Katsina yana neman kotu ta tabbatar masa da cewa shine halastaccen shugaban jam iyyar PDP a Katsina.
Kotu ta saka ranar 18 ga watan Janairu a matsayin ranar fara sauraren karar.
Kafin Shari ar Dan baci shugaban PDP da aka nada a gidan Yakubu lado dake Kano.akwai Shari ar su tsohon shugaban jam iyyar Alhaji salisu lawal uli Wanda take a gaban kotu.
PDP a Katsina ta kasa zama lafiya kamar mai bakin uwa.
Wata majiya ta tabbatar ma da jaridun mu cewa, tsohon dan takarar gwamna a PDP ya fara zafafan maganganu akan wasu manyan yan jam iyyar.
Maganganun da kuma zarge zargen da basu rubutuwa.kuma har sun fara komawa kunnuwan wadannnan manyan.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@www.taskarlabarai.com
07043777779 08057777762