A rana ta Biyu: Mutum Ɗari Biyu sun Amshi Horon Noman Tumatiri da Jarin Iri daga Ahamed Dayyabu Safana

top-news

A rana ta Biyu: Mutum Ɗari Biyu sun Amshi Horon Noman Tumatiri da Jarin Iri daga Ahamed Dayyabu Safana

Zaharddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times

A rana ta biyu kuma ta karshe da aka shirya bada horo na musamman ga Al'ummar Yankunan kananan hukumomi uku da tsohon Dan majalisar Dokokin Tarayyar, Hon. Ahamed Dayyabu Safana ya dauki nauyi.

Kamar yanda aka shirya bada horon a dakin Taro na Star Event Arena dake kan titin zuwa Mani a garin Katsina, a ranar Litinin an bada horo ga mutune dari biyu da suka fito daga yankunan Batsari da Danmusa, a ranar Talata kuma horon yaci gaba da mutanen yankin Safana, inda bayan gama bada horon kowane ya samu shedar horaswa da Kudin Iri Naira Dubu Hamsin-Hamsin.

Abdulkadir Zakka tsohon Dan majalisa Dokokin jihar Katsina, kuma tsohon Kwamishina a zamanin Gwamnatin Aminu Bello Masari ya yi kira ga Dukkanin wadanda suka samu horon da su tabbatar sunyi aiki da abinda aka koya masu, yace "Kunga yanzunnan daga gona nake kuma idan nabar nan gona zankoma Noma shine babban rufin asiri don haka ku tabbatar kunyi aiki da kwarewar da kuka samu" 

Haka zalika Hon. Zakka yaja hankalin 'ya'yan Jam'iyyar APC da su hada kai bisa jagoranci daya a karkashin Dattijo Hon. Ahamed Dayyabu Safana, yace "Safana Ubane wanda yake kishi da son al'ummarsa". Yace "wannan na daga cikin kishi da cigaba da wannan bawan Allah yake jawoma al'ummar yankin shi duk da bashi da wata kujera da aka zabeshi don ita.

Shima a nasa jawabin, wakilin tsohon Dan majalisar kuma Maibawa Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya Shawara akan Ayyuka na Musamman a yanzu, Hon. Ahamed Dayyabu Safana, Alhaji Kabir Dayyabu Safana ya bayyana cewa "Duk da ba zabar Ahamed Dayyabu akai ba matsayin da ya samu a yanzu yafi na zaben, yace a da gajeren hannu gareshi amma a yanzu hannunsa yana iya kaiwa ko ina a Nijeriya, don haka Safana, Batsari, Danmusa zasu ci-gaba da ganin ruwan alheri kamar yanda dama ya saba da hakan.

Sana yayi kira ga jigajigan jam'iyyar kuma cibiyar Siyasar Yankin wato Ahamed Dayyabu da Abdulkadir Zakka, da su bawa mara da kunyi su rike yankin da siyasar yankin kada wata baraka ta kara shiga tsakaninsu.

Kamar ranar farko mutane dari biyu suka samu Tallafin na Naira dubu hamsin hamsin inda suka yaba da Addu'a ga Hon. Safana.