SARAUTAR BARDE KERARIYA KATSINA.
- Katsina City News
- 01 Jan, 2024
- 617
Tsarin mulki ko kuma Sarautu a Kasar Katsina ya samo asaline daga mulkin Habe, Wanda Muhammadu Korau, Sarkin Katsina (1348-1398) ya shinfida bisa tsari. Wannan tsari na Sarauta tun daga wancan lokacin ya faro, Wanda aka samu Sarautu, da suka shafi na Yayan Sarki, Bayin Sarki, Sanaoi da sauransu.
Acikin karni na (19), lokacin da Ummarun Dallaje ya zama Sarkin Katsina (1806) ya kirkiri sabbin Sarautau da Kuma aro wasu Sarautun daga Kasashen Hausa da sauransu.
Sarautar Barde Kerariya tana daya daga cikin Sarautun da Masarautar Katsina ta aro daga Masarautar Kano, a lokacin Mulkin Sarkin Katsina na yanzu, Alhaji Dr. Abdulmumini Kabir Usman. A Masarautar Kano, Sarautar Barde Kerariya tana daya daga cikin Sarautu na Yayan Sarki.
Da Mai Martaba Sarkin Katsina Dr. Abdulmumini Kabir Usman ya aro wannan Sarauta Sai ya nada Alhaji Murtala Ibrahim Safana a matsayin Barde Kerariya Katsina.
An haifi Alhaji Murtala Ibrahim Safana a shekarar (1960) a Masarautar Katsina. Bayan ya kammala karatun shi na Firamare, ya halarci Makarantar gaba da Firamare ta Koyan Sanaoi ta daga shekarar (1973-78) sannan Kuma ya halarci Makarantar Kimiyya da Fasaha, ta Zaria (1978-80) watau Katsina College of Arts, Science and Technology, Zaria. Ya samu Digiri din shi na farko akan Land Survey a Jamiar Ahmadu Bello ta Zaria a shekarar (1983) da Kuma Digiri na (2) ( Masters) degree Akan Land Survey a shekarar 1990. Yayi kwasa kwasai da dama da suka da certificate akan computer a Kasar Sudan. Yayi ayyuka wurare da dama a Tsohuwar Gwamnatin Kaduna daga shekarar 1984-1987, Wanda daga baya bayan an Kirkiri Jihar Katsina a shekarar 1987, ya dawo da aiki a Jihar Katsina. Ya zama Acting Assistant Surveryor General a tsawon shekaru da dama a Jihar Katsina Wanda daga baya ya bar Jihar Katsina , ya koma aiki a Federal Capital Development Authority Abuja a shekarar 1992.
Alhaji Murtala Ibrahim Safana yayi halarci kwakwasai da dama da suka shafi aikin shi, sannan Kuma ya rubuta kasidu da dama na ci gaban al'umma. Alhaji Murtala Safana Yana daya daga cikin Yan Takarar Sarkin Katsina da suka fito daga Gidan Dallazawa, bayan rasuwar Mariganyi Mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Dr. Muhammadu Kabir.
Sarkin Katsina Alhaji Dr. Abdulmumini Kabir Usman ya nada shi Sarautar Barde Kerariya Katsina.
Alhaji Musa Gambo Kofar soro.