"Gwamnatin Dikko Radda Ta Ci Moriyar Musulunci Fiye da Gwamnatocin Baya" -Abu Ammar Sabon Kwamandan Hizbah
- Katsina City News
- 19 Dec, 2023
- 733
Ba'a taɓa gwamnati a Katsina da Musulunci ya ci moriyar ta ba irin ta Dikko Umar Raɗɗa - Kwamandan Hisba
Daga Muhammad Kabir, Katsina
A kokarin ta na tsaftace jihar Katsina daga mummunar kaba ira, hukumar Hisba a jihar Katsina, tace zasu dinga yawo da bulala don hukunta masu ɓarna.
Sabon kwamandan hukumar Hisba na jihar Katsina, Sheikh Aminu Usman Abu-ammar ya faɗi haka ne a lokacin da yake karɓar bakuncin kwamandan ƙungiyar Hisbah ta ƙasa Lajnatul Hisbah Association Malam Khamis Abubakar Imam, a ofishin sa dake a jihar.
"Muma zamuyi yawo da bulala, in ta kama ayi hukunci, gwamnati ce zamu yi hukunci. Ba an kafa hukumar Hisba ba ne don a riƙa musguna ma mutane"
"Aikin Hisba ba ge waye gidajen baɗala bane ko gidajen giya ba, zamu dinga shiga kasuwanni da bada hannu a saman hanya."
Daga karshe ya gode ma Gwamnan jihar Katsina, akan namijin kokarin da yayi na samar da hukumar.
Yace tunda akai jihar Katsina, ba'a taba gwamnati a jihar da Musulunci ya ci moriyar ta ba irin gwamnatin Malam Dikko Umar Raɗɗa.
"Malam Dikko Umar Raɗɗa ya cancanci addu'a ta musamman akan nuna damuwarsa da yayi akan Addinin Musulunci."
Kuma ya bada tabbacin yin aiki tare ga dukkanin masu so a kawu gyara a cikin jihar Katsina.
Shima a nashi jawabin kwamandan ƙungiyar Hisbah na ƙasa Malam Khamis Abubakar Imam yace sunyi matukar farin ciki da samar da hukumar a jihar.