Gwamnan jihar Katsina Dakta Radda ya ziyarci wasu muhimman wurare a kasar Turkiyya
- Katsina City News
- 27 Aug, 2023
- 713
Gwamnan Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya ziyarci muhimman wurare a kasar Turkiyya da za su tallafi jihar Katsina ta ci gaba
Mai Girma Gwamnan jihar Katsina tare da kwamishinan lafiya na jihar, Hon Bashir Gambo Saulawa sun kai ziyarar aiki a kamfanin Submed da ke birnin Istanbul na kasar Turkiyya. Kamfanin Submed dai, ya shahara wajen sayar da magunguna da kayan amfanin asibiti masu inganci.
Wannan ziyara ba ta rasa nasaba da kudirin Malam Dikko Umaru Radda na samar da ingantaccin kayan aiki da magunguna a asibitocin jihar Katsina domin kula da lafiyar al'umma a zamanance kuma cikin nagarta da aminci.
Dama dai, gwamnatin Malam Dikko Umaru Radda ta yi alkawarin aiki ba gajiyawa domin inganta sashen kiwon lafiya da zai iya karade al'ummar jihar a dukkanin matakai.
Gwamnatin Malam Dikko Umaru Radda na aiki ba dare ba rana domin farfadowa tare inganta sassan kula da lafiya a matakin farko, ganin cewa ta nan ake baro bide baya, ta yadda al'umma tun daga tushe za su san gwamnatin Katsina karkashin jagorancin Malam Dikko Umaru Radda na da kyakkyawan kudiri na samar da lafiya ga kowa da kowa.
Dama dai, sashen kula da lafiya na a sahun gaba a bangarorin da Malam Dikko Umaru Radda ya sha alwashin ingantawa domin al'ummar jihar Katsina su samu damar a kula da lafiyarsu yadda ya dace.
Kazalika, Malam Dikko Umaru Radda a kasar ta Turkiyya, ya ziyarci wasu asibitocin da suka shahara wajen wankin koda da sauran ayyukan da suke da sarkakkiya na kula da lafiya.
SSA Isah Miqdad
27/8/2023