Jerin amfani 10 da naman Akuya ke yi a jikin mutum da ya hada kara karfin garkuwan jiki.

top-news


Daga Saliadden Sicey 

Mutane da dama musamman a Arewacin Najeriya basu damu da cin naman Akuya ko bunsuru ba.

Da dama ma har kyamar naman suke yi domin a ganin su naman bashi da dadi.

Mutane sun fi harka da naman Sa, Rago ko tunkiya inda haka yasa kasuwan naman akuya baya ja musamman a Arewa.

Duk da haka wasu daga cikin mutanen da suka dandana naman sun tabbatar cewa naman na da dadin gaske musamman idan ya ji kayan hadi.

Sun ce naman kan yi dadi idan aka yi farfesu ko kuma aka soya shi ana ci da yaji.

Dakta John Abraham ya tsakuro wasu daga cikin amfanin naman Akuwa a wani bincike da yayi.

Ga amfanin da naman akuya

1. Naman akuya na kare mutum daga cututtukan dake tagayyara zuciyar mutum ba tare da ya sani ba.

Naman akuya na dauke da sinadarin B12, Potassium wanda ke taimaka wa wajen motsa jini da hana bugawar zuciya na farad daya.

2. Naman akuya na hana kiba a jiki.

Kamar ya da mutane ke gudun cin naman sa saboda guje wa kiba cin naman akuya na rage kiba.

Bayanai sun nuna cewa naman akuya na dauke da ‘Saturated Fats’ wanda ke ya Hada da rage kiba a jiki.

3. Yana kawar da damuwa

Naman akuya na dauke da sinadarorin dake kaifafa kwakwalwa, ya hana yawan mantuwa saboda sinadarin ‘Iron da Folate’ dake cikin naman .

4. Yana kawar da cutar daji

Naman akuya na karewa da kawar da cutar daji a jikin mutum domin yana dauke da sinadarin ‘Vitamin B complex’

5. Yana kawar da laulayin haila

Naman akuya na hana mata saurin fushi, Da damuwa sannan yana kau da laulayin haila ga mata.

6. Yana hana haihuwan jarirai da nakasa

Naman akuya na dauke da sinadarin ‘Iron wanda ke inganta girman jikin jariri,Vitamin B12 wanda ke kara jini a jiki, sannan da ‘Calcium’ wanda ke kara karfin kashi.

7. Yana taimakwa wajen kawar da cutar siga

Naman akuya na dauke da Vitamin B, yana kuma hana kiba a jiki sannan yana dauke da Protein wanda ke gina jiki.

8. Yana kara wa namiji karfi gaba

Naman akuya na dauke da sinadarin kara garkuwan jiki da faranta wa mutum zuciya yana kara wa namiji karfin gaba wajen yin jima’I.

9. Naman akuya na hana saurin tsufa – Adadin sandarorin da ke kunshe cikin nama Akuya, yakan hana sa jikin mutum ya nuna tsufa.

10. Idan aka jure cin naman Akuya mace mai son yawan gashi zai fito sannan ya kara tsawo. 

Sannan kuma ya na sa a rabu da yawan bushshewar fata kurarraji, Kyasfi da sauransu.

Toh Kunji Fa

NNPC Advert