Ambaliyar ruwa ka iya shafar wasu jihohi takwas a Najeriya masu makwabtaka da kogin Lagdo
- Katsina City News
- 27 Aug, 2023
- 617
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Najeriya, NEMA ta lissafa Adamawa, Edo, Kogi, da wasu jahohi 8 da ambaliyar ruwa zata shafa a yayin da Kamaru ke yunkurin buɗe madatsar ruwa ta Lagdo.
Daga Hassan Abubakar Ahmad Katsina.
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta lissafa jihohin Najeriya da ke ƙarƙashin kogin Benue da ka iya shafa sakamakon sakin ruwa daga Dam Lagdo da ke Kamaru.
Ma’aikatar ta samu sanarwa daga babban hukumar Jamhuriyar Kamaru da ke sanar da cewa jami’an ƙasar za su buɗe kofofin ruwa na Dam Lagdo da ke gabar kogin Benue nan da kwanaki masu zuwa.
A cikin wata sanarwa da shugaban sashen yada labarai na NEMA a Abuja, Manzo Ezekiel ya fitar, hukumar ta ce tana aiki tare da masu ruwa da tsaki na tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi don tabbatar da cewa sakin ba zai haifar da mummunar illa ga masu ƙaramin ƙarfi ba. Tare da jihohin da abin ya shafa".
Ya lissafa jihohin da ke gefen kogin Benue a matsayin "Adamawa, Taraba, Benue, Nasarawa, Kogi, Anambra, Enugu, Edo, Delta, Rivers da Bayelsa".
"Hukumar ta yi hasashen wannan sakin ruwa mai yawa daga madatsar ruwa ta Lagdo, tare da lura da tasirin da zai iya haifar da kuma yin la'akari da shi a shirye-shiryen ragewa da kuma mayar da martani ga faɗakarwar ambaliyar ruwa na 2023," in ji ta.