"Za'a Shimfida Tituna a wasu Muhimman Unguwanni Uku a Karamar hukumar Katsina" Inji Honorable Danlami
- Katsina City News
- 16 Dec, 2023
- 607
"Za'a Shimfida Tituna a wasu Muhimman Unguwanni Uku a Karamar hukumar Katsina" Inji Honorable Danlami
Zaharaddeen Ishaq Abubakar,
Sani Aliyu Danlami Dan Majalisar Wakilai ta Tarayya a karamar hukumar Katsina ya bayya cewa Zaya Shimfida Tituna a wasu Muhimman Unguwanni Uku a cikin garin Katsina, Titunan sune a Unguwar Tashar Rabe, Kofar Sauri zuwa Lambun Danlawan, da Kuma Layout wajen sabon gari Police Station.
Honorable Danlami ya bayyana haka a lokacin kaddamar da gina Rijiyoyin Burtsatse guda 100, da Fitilu guda 150 masu amfani da hasken rana a karamar hukumar Katsina.
Taron bude fara gina Rijiyoyin da fitilun da ya gudana a Unguwar Modoji a Kofar gidan Uban jam'iyyar APC na jihar Katsina Alhaji Sule Yari ya samu halartar 'Yan Siyasa na Karamar hukumar Katsina, Hon. Aliyu Abubakar Albaba, Engr. Muttaqa Rabe Darma, Alhaji Sule Yari, Alhaji Sabo Musa Hassan, Shugaban Hukumar Tsaftace gari (SEPA) na jihar Katsina, masu taimakawa Gwamnatin jihar Katsina a Fannoni daban-daban da sauransu.
A jawabinsa wajen taron Engr. Muttaqa Rabe Darma yayi bayani ta yanda aikin rijiyar Burtsatsen kai tsaye ta kawo sauki da samun kudin shiga a akalla naira bilyan biyu a shekara.
Alhaji Sule Yari ya sha alwashin sa ido da kula da fitilu da rijiyar da ke yankinsa, sana yayi kira da sauran al'ummar karamar hukumar Katsina da suma su kafa wani kwamiti da zai lura da wadannan abubuwa na ci-gaba.
Honorable Sani Aliyu Danlami ya bayyana cewa wadannan Ayyukan 'yan Kadanne daga cikin gurinsa dama wasu ayyuka da nan gaba kadan zai bayyana su idan sun zo hannu, ya kuma ce zaya samarwa matasa ayyukan yi, kamar yanda yayi a baya saboda kujerar ba bakuwa bace a wajensa. Danlami yayi alƙawarin bada jari ga mata masu ƙananan sana'o'i da matasa a karshe ya nemi addu'a da goyon baya ga 'yan karamar hukumar Katsina.