Tinubu Ya Cire Malaman Jami'a Daga Tsarin Albashin Na IPPIS
- Katsina City News
- 13 Dec, 2023
- 488
Majalisar zartarwa ta Najeriya ta cire malaman jami'a, da na kwalejojin ilimi da fasaha daga tsarin albashi na Integrated Personnel Payroll Information System (IPPIS).
Ministan Ilimi Farfesa Tahir Mamman ya ce Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ne ya ba da umarnin yin hakan a zaman majalisar da ya jagoranta a yau Laraba.
Ya ƙara da cewa hakan zai bai wa shugabannin cibiyoyin ilimin damar ɗaukar ma'aikata ba tare da sun nemi amincewar ofishin shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya ba.
"A taƙaice, shugaban ƙasa da majalisar sun nuna damuwarsu ne kan yadda ake gudanar da jami'o'in, amma hakan ba shi da alaƙa da zaɓar wani tsarin biyan albashi ko kuma zargin rashin adalci," a cewar ministan kamar yadda kafofin yaɗa labaran Najeriya suka ruwaito shi yana faɗa jim kaɗan bayan kammala zaman a fadar shugaban ƙasa.
Ƙungiyar malaman jami'a ta ASUU ta daɗe tana neman gwamnatin Najeriya ta cire su daga tsarin, wanda ya hana su gudanar da wasu ayyuka da kuma ƙayyade kuɗin da za su samu a matsayin albashi.
Hakan na nufin yanzu jami'o'in da sauran kwalejoji za su dinga biyan malamansu albashi da kansu ba sai sun dogara da gwamnatin tarayya ba, in ji Ministan Yaɗa Labarai Muhammed Idris