Tarihin Unguwar Marnar Gangare a cikin Birnin Katsina

top-news

Tarihin Unguwannin Katsina 

MARNAR GANGARE

Zaharaddeen Ishaq Abubakar 

Marnar Gangare tana nan tsakanin Unguwar Yari da Sagi. Dalilin da ya sa ake kiran Unguwar da wannan suna shi ne kasancewar wurin da marinar take gangare ne. Saboda haka domin a banbata da sauran marinun da ke cikin Birnin Katsina, sai mutane suka sanya mata suna 'Marnar Gangare. 

An kafa Marinar Gangare tun lokacin mulkin Habe a Katsina. A zamanin da ana rina kayayyakin gargajiya iri-iri a Marnar Gangare. Baya ga rini, marnar tana samar da katsi domin shafen gidaje. 'Shi Katsi kamar siminti yake". 

Wata majiyar tarihi ta nuna cewa a da, ana samun katsi da ake amfani da shi wajen shafen Gidajen masu hannu da shuni na garin Katsina.

Marnar Gangare ne ake samun Katsi da ake shafen gidan mai Martaba Sarkin Katsina, da kuma gidajen Turawa a Bariki, watau (GRA) da aka gina.

Tarihi ya nuna cewa Marnar Gangare daga wurare daban-daban ne suke kawo kaya kuma su sari kayayyakin da aka rina a Marnar gangare. Baya ga kayayyakin saki, ana kuma rina zare da sauransu akai kasuwar Kaita da Jibiya a sayar da shi ga masaka, su kuma su yi amfani da shi wajen saka kayayyaki kala-kala.

Wasu daga cikin tsofaffin marinan marnar gangare sun hada da, Malam Ali da Malam Salele da Malam Abu da Malam Sani da Malam Hamisu da Umar da Yakubu da Salisu Dugunsa da Jari da Alhaji Danmare wanda shi ne mutum na Karshe da ya yi rini a Marnar Gangare. 

An bar rini kwata kwata a marnar gangare wajen shekara ta 2000. A halin yanzu wannan marnar babu ita domin tuni aka cike ta. Filinta yana nan tsallaken hanya kudu kadan da gidan Alhaji Ali Mai Chanji. (Ko da yake anyi wasu gine-gine da masallaci a wani bangaren wajen tare da Kanikawa da masu walda suke zama wajen) 

A shekarun da suka wuce wannan Unguwa ta Marnar Gangare cibiya ce inda ake sayar da kayayyakin gargajiya.

An yi wani mutum wanda ake kira da suna Zaki' a Marnar Gangare. Wannan mutum shi ne wanda yake sayar da wadannnan kayayyaki a cikin makeken shago. Kayan sun hada da tukwane, korai, fayafai da sauransu. Zaki ya shahara kwarai a garin Katsina mafi yawancin abokan huldarsa mata ne. Idan azumin watan Ramalan ya zo, yara samari da mata Sukan yi tururuwa zuwa shagonsa domin sayen kayayyaki. Yara sukan sayi Talle suyi amfani da shi wajen wasannin tashe. Su kuma mata su sayi Tukwane da Korai domin kaɗa kunu da koko. 

Kamar sauran ungunni Marnar Gangare tana da tsoffin 'Yan kasuwa irin su Alhaji Dankundakushi, da Alhajı Barau Mai Fanka, da Alhaji Abdu Yarsoda, da Hamisu Dan Maiyawo, da Alhaji Sani, da Alhaji Malam Abdu, da Alhaji  Ali Mai Chanji da Alhaji Abdu Taki, da sauransu. 

Haka  kuma akwai tsaffin Malamai irin su Alhaji Muntari Dan Jana, Alhaji Malam Tasi'u, Alhaji malam  Misha, da Alhaji Dillo, da Alhaji Tukur, da Alhaji Iliyasu, da Alhaji Malam Rufa'i, da Alhaji Malam Usman, da Malam Bishir, da Alhaji Malam Kalla da dai sauransu su.

Mun ciro daga Littafin Tarihin Unguwannin Birnin Katsina da kewaye wanda Hukumar Binciken Tarihi da kyautata Al'adu ta jihar Katsina ta Wallafa.