DALILAN DA YASA ECOWAS KE NEMAN YAQI DA QASAR NIGER - Tsaraba ga Masu Ziyarar Sheikh Zakzaky
- Katsina City News
- 26 Aug, 2023
- 667
Duk da Takunkumin da Europe da USA suka sanyawa Russia. To har yanzu USA daga Russia take sayen Uranium. Bata saka mata Takunkumi a nan ba. Idan ta saka mata Takunkumi to za ta rasa isasshen Uranium. Kodayake ba a hannun Russia kawai suke saye ba, suna kuma saye daga Uzbekistan. Sai dai inda matsalar take shine dole sai sun biyo dashi ta Baqin Teku(Black Sea), Wanda kuma Russia ke tafiyar dashi. Don hakane suke neman wata Qasar da za ta maye Gurbin Russia wajen samun Uranium.
To Qasar Niger ce kawai ta cika wannan Sharaɗin. Wadda France ta mamaye, wadda kuma ke baiwa Europe kimanin 35% na Uranium din da suke Buqata.
USA na cikin qoqarin yiwa France wayo ta amshe Niger ta hanyar Bazoum, kwatsam sai ga Juyin mulki. Juyin Mulkin da Jagororinsa suke neman RUSSIA ido rufe akan ta zo Niger ta dafa masu. Wato kenan yanzu da Uranium din Russia Dana Uzbekistan Dana Niger, kimanin 50% kenan na Uranium din Duniya, duk ya faɗa a hannun Russia. Hakan ya bar USA da Europe da Zaɓi 3 kacal :
Na farko kodai su cigaba da saye daga Russia ko kuma su qwaci na Niger daga hannunta da karfi, ko kuma su zauna ba Uranium.
Don haka sai sukaga hada Yaqi a Niger Republic shine abu mafi Sauqi a wajensu. Kodai yaqi ko tada rikicin Qabilanci, Tsakanin Kudanci da Arewacin Niger din. Batun Uranium shine qaramin Dalili.
2. Babban Dalili kuma shine batun samun Iskan Gas. Kafin Yaqin Ukraine, man ma kusan Russia ce ke baiwa gaba ɗayan Europe Iskan Gas. Lokacin da yaqin ya balle su da kansu suka bari USA ta fasa bututun Gas ɗin na cikin Teku, wai su wautarsu za su karya Tattalin arziqin Russia ne idan sun bar sayen Gas dinta.
Basu san Shugaba Putin ya fisu iya Tsiya ba. Kafin ya fara Yaqi a Ukraine sai daya tsara komai, daga ciki akwai yanke kowace Alaqar Kasuwanci da Turai, kuma ya nemi makwafinsu a wata Nahiyar, amma sai ya bari su su fara yankewa da kansu. Suna yankewa kawai sai yayi sauri ya qulla yarjeniyoyi da wasu Qasashen irinsu India, China, Indonesia, Iran dss. Maimakon Russia ta cutu sai ta qara qarfi. Su kuma Europe suka shiga wahala.
To dama tun 1970 akwai batun suna son su janyo bututun Gas daga Nigeria zuwa Europe. Wanda zaibi ta Niger da Algeria. Daga nan a raba shi biyu Ɗaya ya shiga Italy daya kuma Isfaniya. Abunda ya hanasu tun tuni shine suna samun na Russia kuma da Arha.
To yanzu sun fasa Bututu(Nord stream) da kansu. Kuma suna Dandana kuɗarsu. Shine a watan July na shekarar da ta wuce, suka dawo gadan-gadan suna ta aikin saka Bututun Iskan Gas daga Kudancin Nigeria zuwa Niger da Algeria. Dama tun a 2010 sun fara aikin. Amma yana tafiyar Hawainiya. An qiyasta cewa yanzu har sun kashe Kuɗi fiye da $13b.
Duk wanda ke bin Hanyar Abuja zuwa Kano a Shekarun nan zai ga ana wucewa da manyan pipes ana ratsa Daji ana shimfida su a Qasa. Shi wannan aikin duk wasu Kidnappers ko Bandits basu isa su hana yinsa ba.
Suna cikin haka kwatsam sai ga Qasar Niger na neman kubce masu, ta koma hannun Russia.
Domin Sojojin da sukayi juyin mulki sunce ba ruwansu da Yarjejeniyar da aka yi a 2003 da 2006 game da aikin a Algeria. Su sun fita. Idan Niger ta fita to babu aikin kenan.
Idan kuma babu aikin To Europe da France suna tsaka mai wuya game da samun Iskan Gas, wanda yanzu haka mai tsada suke saye daga USA. Ita kuma Russia tana son ta gallaza musu ta Takura musu, ta gasa musu Aya a hannu. Kenan fara yaqi a Niger zai zamo na qwatar kaine, don haka zai yi muni.
3. Idan sun fara yaqi, dama a wajensu mu Africa ba mutane bane. Gara mutanen Ukraine ana cewa su fita gari kafin a gwabza. Mu share mu za su dinga yi, ba tausayi. Gas ya fimu daraja a wajensu. Dalar da suka zuba ta fimu Daraja.
Da suyi Asarar Dala Biliyon 13 gara su kashe kowa, musamman idan kowan nan Musulmin Niger da Najeriya ne. Shi yasa yaqin zai yi muni fiye da na Ukraine.
Yanzu kodai Qasar Niger tayi sulhu dasu, a bar Bututunsu ya tafi. Ko kuma Su kunna Yaqi gadan-gadan tsakanin ECOWAS da Sojin Niger, ko kuma ‘Yan tawayen Arewacin Niger su dauki makamai, da niyyar dawowa da Bazoum, a Kudanci kuma a turo masu ISIS da Boko Haram. Ana kashemu suna kwasar Uranium, Bututunsu na yana tafiya babu matsala.
To yanzu meye abun yi?
Na farko Komawa ALLAH SWT da Addu’a. Na wayar da kan mutane, ta hanyar gaya musu Asalin matsalar su. Na Ukku Matsawa hukumomi Lamba a kan ba’a yadda da yaqi ba.