“Tsananin Yunwa a Najeriya Matan Aure na bada kansu ga Maza don su sayi Abinci- inji Mahdi Shehu
- Katsina City News
- 26 Aug, 2023
- 698
Daga Zaharaddeen Gandu
Mahadi Shehu yace da yawan wasu Matan Aure maza na amfani da su domin su samu kuɗin da za su rinƙa siyoma Yaran da suka haifa Abinci saboda mazajen ba su da kuɗin da za su ciyar da su saboda yunwa.
Ɗan asalin jihar Katsina Ɗankasuwa mai jerin kamfanonin Dialogue Dr. Alhaji Muhammadu Mahadi Shehu, ya bayyana Hakan a shafi sa mai suna Rescue Arewa Urgently, a ranar Asabar 19 ga watan Agustan 2023.
Tun da farko yace akasarin Malam Arewacin Najeriya ɗaiɗaya ne ba su fito suka hau mambari suka faɗawa mabiyansu su zaɓi Bola Tinubu, yace saboda rashin Adalci amma yunwa ta addabi al'ummar Najeriya musamman Arewa amma daga cikin su babu wanda ya bada shawarar suje wajensa su faɗa masa halin da al'ummar Najeriya suke ciki na fatara da yunwa da kuma ƙuncin Rayuwa saboda kar a daina ba su abinda ake ba su a ɓangaren gwamnatin sa.
Yayi nuni da cewa, saboda matsalar yunwa da ake fama da ita Matan Aure akasarisu su ke cida mazajensu da yaransu ta hanyar bada kansu ga Maza a waje domin basu da hanyar da za su samu kuɗin da zasu ci Abinci idan ba ta wannan hanyar ba musamman a Arewacin Najeriya.
A cewar sa, wata da bakinta ta faɗa masa cewar ƙawarta tashiga damuwa sakamakon sai ta bada kanta take samun kuɗin da take ciyar da kanta da yaranta da mijinta, inda daga ƙarshe ta faɗawa mijinta sai ta bada kanta take samun kuɗin da take ba shi domin ba aiki take zuwa ba kamar yadda tai ma sa ƙarya a baya, sai mijin yace ya yafe mata duk abinda ta aikata da wanda take shirin yi domin yasan halin da suke ciki.
Mahadi Shehu ya tunatar da Malaman cewa, kamar yadda suka je Nijar suka bayar da shawarar kar ayi yaƙi, yana kira garesu da su je fadar shugaban ƙasa Bola Tinubu su faɗa ma sa halin da ya jefa Al'ummar Najeriya kuma kar su ji tsoron faɗa masa haka. Yace idan suka kasa faɗa masa gaskiya Allah zai tambaye su kuma al'umma za su yi masu mummunar fassara musamman a lokacin da suke hawa kan mumbari suna ma shi kamfen.
Kazalika ya ƙara da cewa, da yawan Malaman sun rinƙa fatawar duk wanda bai zaɓi Bola Tinubu ba bai cika Musulmin ƙwarai ba ta haka suka ja ra'ayin mabiyansu domin zaɓen sa. Amma ga shi ko wata 4 ba a yi ba a mulkinsa yunwa ta addabi al'ummar ƙasar da tsadar rayuwa, saboda son duniya Malaman sun kasa faɗa masa gaskiya don kada ya yanke kuɗin da yake ba su da kuma tikitin zuwa Makka da Umarah da sauran ƙasashen ƙetare.
Ya bayyana cewa, ko maƙiyin Allah da Manzonsa yasan yunwa ta kai yunwa, fatara ta kai fatara wanda zaka ga miji ya gudu ya bar Matarsa da yaransa da danginsa saboda masifar yunwa domin bai da abinda zai ciyar da su shi ma yunwar ta addabe shi.
Ya jaddada cewa, kodayake talaucin da ake fama da shi bai shafi 'ya'yan su da matansu ba shiyasa basu damu da abin da al'umma ke ciki ba. Yace kar su manta akwai ƙin-randillanci domin arziki bai dawwama haka talauci ma bai ɗorewa kuma rayuwa ba ta da tabbas.