KADAN DAGA CIKIN SARAUTUN DA AKA KIRKIRA, BAYAN KAFUWAR DAULAR USMANIYYA A SOKOTO(1804).
- Katsina City News
- 07 Dec, 2023
- 1476
Bayan an kare Jihadin 1804, a Sokoto, sai Shehu Usman Danfidio( Mujadadi) ya umarci shugabanni Jihadi dasu kirkiri Sarautar wadanda zasu taimakamasu wajen tafiyar da tsarin mulki na musulunci a Daular Usmaniyya. Kamin Jihadin Shehu a shekarar 1804 Sarakunan Habe na Kasar Hausa sun kawo tsarin Sarautar Gargajiya ta Hausa a Kasar Hausa. Daga cikin Sarautun da aka kirkira a Daular Sokoto bayan an kare Jihadi akwai 1. Sarautar Waziri 2. Da SAI da kuma 3. Sarautar Sardauna.
1. Sarautar Waziri. Ita Sarautar Waziri an fara tane a Sokoto bayan an kare Jihadi. Babban aikin Waziri a Daular Usmaniyya shine yaba Sarkin Musulmi shawarwari wajen tafiyar da mulkinshi, sannan kuma yana kula da kuma shugantar gyara ko kuma sake ginin ganuwar Sokoto, cibiyar Daular Usmaniyya, da kuma Masallatai da sauransu. Waziri na farko a Daular Sokoto lokacin mulkin Sarkin Musulmi Muhammad Bello shine Gidado dan Laima, kuma shi babban abokin Sultan Muhammadu Bello ne, domin a lokacin da ake gudanar da Jihadi shine a matsayij lieson officer tsakanin Sultan Bello da Shehu Danfodio.
2. Sarautar SAI. Ita wannan Sarauta ta SAi an kirkiretane a Daular Sokoto bayan an kare Jihadi. Babban aikin SAI shine ansar Zakka ga masu iko. Zakka ba kamar Sadaka bace, ita dole ce, SAI shi.zai zagaya gari ya tabbatar da cewa duk wani mai iko ya bayar sa Zakka. Mutum na farko da aka fara nadawa SAi shine SAi Maituta, a lokacin mulkin Sarkin Musulmi Muhammad Bello.
3. SARAUTAR SARDAUNA.
Sarautar Sardauna ta samo aslintane a Sokoto lokacin mulkin Sarkin Musulmi Muhammad Bello (1817-1837). Sultan Muhammad Bello ya aro wannan Saraura ta Sardauna daga tsohuwar Daular Gobir ta Kasar Hausa, bayan an kare Jihadin Shehu Usman Danfodii na karni na 19. Mutum na farko da aka fara nadawa Sardauna a Sokoto shine Malam Halilu dan Malam Hassan dan Mujadddadi Shehu Usman Danfodio, wanda Sarkin Musulmi Muhammad Bello ya nadashi.
Musa Gambo Kofar soro.