WASIKAR WATA BAYAHUDIYA DAGA CIKIN WADANDA HAMAS TA SAKI
- Katsina City News
- 28 Nov, 2023
- 810
Zuwa ga Janar din da ya rako ni a makwannin da ya shige, Ina ganin gobe ne zamu rabu. Don haka Ina gode maka daga karkashin Zuciyata, saboda tsananin tausayawar da ka nunawa 'Ya ta, Emilia.
Ka zame mata tamkar mahaifi, kana gayyatarta dakinka a duk lokacin ta bukaci Hakan.
Ta tabbatar da yadda dukkanku ku ka dauketa tamkar Kawarku. Cikin kauna da kyautatawa.
Ina godiya, Ina godiya, Ina gode Maka na tsahon sa'o'in da ka dauka a matsayin mai lura da mu.
Ina gode maka na hakurin zama da ita da yadda aka dinga bata alewa, kayan marmari, da duk abin da yake akwai har a lokacin da babu.
Yara bai kamata su zama tsararru ba .Amma Ina gode maka da kai da sauran Mutanen masu kirkiri da muka hada su akan hanya. 'Ya ta tana Jin tamkar Sarauniya ce a GAZA...
Tana godiya gabadayan yadda ta zama kamar wata Duniya da babu kamar ta. Ba ta hadu da wani ba a tsahon tafiyar da muka yi tun daga kan mai mukami na karshe har zuwa Jagoran babu wanda bai nuna mata kauna da tausayawa da soyayya ba.
Dole na zama mai dauke da bashin godiya, saboda ba ta bar wajen nan da dauwamaman firgici a zuciyarta ba. Zan tuna da kyawawan halayenku, da ku ka nuna a nan duk da tsananin yanayin da ku ke fama da shi da irin munanan asarar da ku ka yi a a nan Gaza.
Na yi fatan a ce a wannan Duniyar za mu zama Abokai na gari.
Ina muku fatan alheri da kwanciyar hankali... Lafiya da kauna ku da Iyalinku. Godiya mara adadi.
Danyal da Emilia.
Danyal and Emilia"
Mun dauko daga shafin Ibrahim Daurawa kano