Resource Forum Karkashin Jagorancin Sheikh Zakzaky ta shirya Taron Lakca akan Falasdinawa da gudanar da Addu'o,i na musamman.
- Katsina City News
- 25 Nov, 2023
- 1827
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Resource Forum Karkashin Jagorancin Sheikh Ibrahim El-zakzay, reshen jihar Katsina sun gudanar da taro akan halin da Falasdinawa suke ciki da yin Addu'o,i na musamman don kara samun nasarar yakin da suke da Yahudawan Israel.
An gudanar da taron lecture a ranar Asabar 25 ga watan Nuwamba 2023 dakin taro na Katsina Multipurpose Women Center dake filin samji cikin Birnin Katsina.
Taron wanda ya kumshi kasidoji mabambanta daga bakin Doktoci manazarta masana Tarihin Duniya da suka dade suna koyarwa a jami'o'in jihar Katsina, wanda tun a farko shugaban Forum din Engr. Hamisu Imam ya gabatar da makasudin shirya taron.
Engr. Hamisu ya bayyana cewa "Makasudin shirya wannan taron shine Tunatar da juna da kuma Jajantawa akan mu, bisa lamarin da yake faruwa a Duniya na yakin Kasar Falasdinu da Israel." Yace "Al'amarin Falasɗinu ba na Musulmi kadai bane na Dukkanin Dan Adam ne, wanda yake da ruhin Tausayi da Jinkai, saboda abin ya shafi 'Yan'adamtaka." Yace "don haka muka gayyato Mutane ma bambanta ra'ayi da fahimta, da kuma Addini saboda manufar daya ce, itace haduwa domin nuna Dan-adamtaka Tausayi da kuma Addu'a ta Musamman."
Dokta Abdullahi 'Yar'adua ya gabatar da Lecture mai matukar muhimmanci akan Asalin Yahudawa da kuma su kansu Falasɗinu, ya bayyana dalilan fadan da ya kwashi shekaru masu yawa ana yinsa a tsakaninsu. Yace "An fara fada tsakanin Yahudawa da Falasɗinawa tun a shekarar 1897 da wasu mutane da ake kira Zionist suka bukaci a samar masu kasa da zasu zauna a cikin kasar Falasdinu." Yace Asalin Rigimar kenan.
Dokta Abdullahi 'Yar'adua ya bayyana kasashen da suka mara masu baya wajen ganin an samar masu da mazauni da karfi, inda yace ƙasashe Ingila, Amurika da Faransa, inda yace Kasar Ingila itace ta Ayyana samar da kasar Israel a cikin kasar Falasdinu inda wannan bukata ta kasar Ingila ta samu amincewar Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 1947.
A cikin Kasidar tasa Dokta Abdullahi 'Yar'adua ya bayyana cewa daga nan ne fadan ya soma.
Dokta ya kawo Tarihi na Bincike da kuma hakikanin irin gudunmawar da kasashen Yamma suka bada wajen tauyewa Falasɗinawa 'Yanci na zamansu halastaccin 'Yan kasa.
Shima Dokta Abdullahi Isah Malami a Makarantar Kimiyya da fasaha ta Hassan Usman Katsina ya kawo Tarihin makircin yahudawan Duniya da salon tsarinsu na cusa miyagun Dabi'u ga Al'umma kaitsaye ko kuma ta karkashin kasa.
Dokta Isah yace "Bayahude yana so ya mamaye Duniya ne, yace dama yankin yammacin Duniya suke da shi, amma a haka saida suka shigo yankin Larabawa, da Afrika ta Hanyar shigar da jininsu a jikin Sarakuna, malamai da duk wasu da suke saran zasu iya amfani dasu don yakar al'ummar yankin," yace "ba abin mamaki bane don kaji Bakar fata yana goyon baya ko yana yin aiki irin nasu, domin akwai bakaken yahudawa."
Dokta a cikin Kasidar tasa mai tsawo ya bada Misalai da kuma irin yanda hakikanin halin yahudawa yake ta hanyar dabi'u da Mu'amala.
Kasidar tasa gaba daya ta tataro irin Danniya da Zaluncin da Yahudawa sukewa Falasɗinawa da Musulmin Duniya, da kuma Kalubale dake gaban Musulmi da matakin da Yakamata musulmi su dauka don kaucewa sharrin yahudawa.
Sheikh Isma'il Bin Zakariyya Alkashnawy Malamin Addinin Musulunci ya takaita jawabinsa akan Ayoyin Alkur'ani Mai girma guda hudu da sukai zance akan yahudawa inda a ciki ya fadakar ya kuma tunasar dangane da sharrinsu, Butulcinsu, da Makircinsu, yace duk da a cikinsu akwai mutanen kirki, amma ba a taba wata halitta da tayiwa Allah Butulci kamar Bayahude ba, yace shi yasa ma Alkur'ani mai girma ya fallasasu ya tona masu Asiri.
A karshe Sheikh yayi fatan Alheri ga jagoran harkar musulunci a Najeriya Sheikh Ibrahim El-zakzay da kuma Sheikh Yaqoub Yahaya Katsina.
Da yake taron ya samu halartar Kiristoci, Madam Martha Cosmas Essien ta bayyana Damuwa da juyayin akan halin da Falasdinawa suke ciki tare da yin Addu'o,i na musamman akansu.
Sheikh Usman Dalhatu Karkarku, shine ya wakilci Sheikh Yakub Yahaya Katsina a wajen taron, yayi bayani filla-filla akan yahudawa da Makircinsu, sana kuma ya bayyana farincikinsa akan yanda duniya ta sheda cewa Yahudawan Israel sun gaza kuma sun fadi a yakin da suke da Falasdinawa.
A karshe an gabatar da Addu'o,i na musamman ga bakidaya da nufin Allah ya kara bawa Al'ummar Falasɗinu Nasara.
Taron ya samu halartar: Dokta Abdullahi Isah, Dokta Tukur Usman, Dokta Jamilu Kankia, Dokta Abdullahi 'Yar'adua, Sheikh Isma'il Bin Zakariyya Alkashnawy, Sheikh Usman Dalhatu Karkarku, Mis Matha Cosmas Essien da sauran muhimman mutane da bamu ambata ba.