KOTUN KOLI TACE A BIYA MAJIGIRI NAIRA MILYAN ASHIRIN.
- Katsina City News
- 25 Aug, 2023
- 724
Muhammad Ali @ katsina times
Babbar kotun tarayya dake Abuja ta yanke hukuncin a biya Dan majalisar tarayya mai wakiltar Mashi da Dutsi Alhaji Salisu Yusufu Majigiri naira Milyan ashirin.
A hukuncin da alkalai biyar suka yanke Wanda Babban alkalin alkalan kasa, ya rubuta ta yanke hukuncin cewa, Wanda ya shigar da karar Nazifi MB mashi da kuma lauyan jam iyyar PDP sun yi wasa da hankalin kotu da kuma raina Shari a.kamar yadda yake a cikin Takardar hukuncin da aka karanta a ranar 10/agusta/2023.kamar yadda katsina times ta samu kwafin hukuncin ta kuma Wallafa shi a shafin ta.
Hukuncin yace ga shaida na takardu ingantattu cewa Wanda ya kai karar ya amince da zaben fitar da dan takarar da akayi a ranar 2/7/2022.amma kuma ya shigar da karar zaben fitar da Dan takarar a 25/11/2022.Bayan kundin tsarin mulki cewa yayi a shigar da kara cikin sati biyu.
Hukuncin yace lauyan jam iyyar PDP ya San cewa an saba ma tsarin mulki na shigar da karar da kuma dokar zabe,amma duk da haka ya tsaya domin kariya ga abin da baya da hujja.
Hukuncin yace, don haka,Wanda yayi karar Nazifi MB mashi da kuma lauyan jam iyyar PDP su biya naira Milyan Goma Goma ga Wanda sukayi karar Alhaji salisu Yusufu majigiri.
Katsina times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai
07043777779. 08057777762