Iran ta gabatar da jirgi marar matuƙi da zai iya kai wa Isra'ila hari
- Katsina City News
- 25 Aug, 2023
- 616
Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Husain Dehqan ya kaddamar da wani sabon jirgin sama mara matuki da masanan Iran suka kera wanda kuma aka ce shi ne irin sa mafi girma da kasar ta kera da aka ba shi sunan Fotros da ke da gagarumin karfi na tattaro bayanai bugu da kari kan kai farmaki daga nesa.
Ministan ya kaddamar da wannan jirgin ne a wani biki da aka gudanar a yau Litinin (17-8-2013) inda ya bayyana cewar kafin kaddamar da jirgin sai dai masana suka gwada shi a lokuta da dama sannan kuma a cibiyoyi daban-daban da suke da kwarewa a fagen ayyukan jirage marasa matukan na Iran inda ya ce an sami nasara a dukkanin gwaje-gwajen da aka yin.
Birgediya Janar Dehqan ya kara da cewa masanan kasar Iran da suke aiki a ma’aikatar tsaron ne tare da hadin gwiwan cibiyoyi daban-daban na kasar suka kera wannan jirgin inda ya ce nasarar da aka samu wajen kera jirgin ya tabbatar wa da duniya cewa takunkumi da kuma ci gaba da takurawa Iran ba zai hana kasar ci gaba a dukkanin fagage ba.
Janar Dehqan ya kara da cewa jirgin yana da karfin tashi sama na tsawon kafa dubu 25 sannan kuma zai iya shawagi na tsawon awanni 16 zuwa 30 ba tare da ya sauko ba, kamar yadda kuma yace yana da karfin tattaro bayanai har daga fadin wajen da ya kai kilomita 2000. Har ila yau kuma ministan tsaron na Iran yace baya ga ayyukan tattaro baya, haka nan kuma jirgin yana da karfin kai hari daga nesa don kuwa yana da karfin dauka da kuma harba nau’oi daban-daban na makamai masu linzami.
Janar Dehqan ya kara da cewa daga cikin ayyukan wannan jirgin har da sanya ido kan iyakoki na kasa da kuma na ruwa da bututun man fetur da hanyoyi na sadarwa da wajajen da wata bala'i ta girgizar kasa ko ambaliyar ruwa da sauran ta same su, sannan da kuma aiko da hotunan da yake dauka ga cibiyar da take kusa da shi a daidai lokacin da yake shawagin.
Ministan tsaron na Iran ya bayyana cewar a halin yanzu dai Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kai matsayin dogaro da kanta a fagen irin wadannan jiragen sama marasa matuka na kariya da kuma kai hare-haren soji bugu da kari kan tattaro bayanan sirri.