Mutanen gari sun fafata da barayin daji a yankin Batsari
- Katsina City News
- 18 Nov, 2023
- 1424
MUTANEN GARI SUN FAFATA DA BARAYIN DAJI A YANKIN BATSARI.
Misbahu Ahmad
@ Katsina Times
Ɓarayin daji masu dauke makamai sun kai hari ƙauyen Watangaɗiya, har sun kashe mutum ɗaya kuma sunyi garkuwa da mutum huɗu.
A daren juma'a 17-11-2023 da misalin 10:00pm ɓarayin daji masu garkuwa da satar dabbobi da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa suka kai hari ƙauyen Watangaɗiya dake cikin yankin ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina.
Ɓarayin sunkai harin ne ɗauke da bindigun bature inda suka kutsa kai wani gida suka yi awon gaba da mutane huɗu.
Amma mutanen gari sun kai ɗauki, inda suka bi su da nufin ƙwato mutanen da suka ɗauka, su kuma ɓarayin suka buɗe masu wuta, nan take suka kashe mutum ɗaya mai suna Hamza.duk da haka mutanen sun rika binsu da jifa da ihu wannan ya tsorata barayin suka shiga daji babu shiri ba kuma tare da cimma mummanar nasarar da suka so samu ba.
Dama dai a kwanakin baya ɓarayin sun kai irin wannan harin a ƙauyen har suka kashe mutum ɗaya kuma suka sace masu shanun noma.
Daga lokacin mutanen garin suka daukar ma kansu an gama daukar su kamar wasu tumakai.suka sha alwashin duk zuwan da wasu barayi za suyi sai an fafata.
Mutanen Sunyi roko ga jami an tsaro su rika kawo masu dauki duk lokacin da suka daukar ma kansu fafatawa da barayi.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
07043777779 08057777762