'Yan Bindiga sun Kashe Miji da Mata Wajen Bikon Maida Aure a Katsina
- Katsina City News
- 24 Aug, 2023
- 834
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A daren ranar Laraba 'Yan Bindiga suka shiga wata Unguwa ta tsohuwar Kasuwar 'Yan Barkono a garin Dandume, inda anan take suka harbi mutum hudu, Mutum biyu suka mutu, Mata da Miji, a lokacin da Mijin yazo Unguwar Neman Bikon Matarsa tsautsayin ya rutsa dashi.
Majiyarmu ta sheda mana cewa Mijin yana tsaye a kofar gidansu Matar yana jiran fitowarta, daga makwafta. Fitowarta ke da wuya goye da Ɗansu bata karasa inda yake ba sai suka buɗe mata wuta, inda harsashin ya fita ta jikinta ya samu yaron da take goye dashi, a gefen cikinsa a nan rake ita Allah yayi mata rasuwa.
Haka zalika shima tsohon Mijin nata da yazo biko kafin ya farga da abinda ke faruwa suka yimasa harbi uku a kirji, da hannunsa anan take ya Mutu, a yayin da kuma suka harbi wani da yazo wucewa a ƙafa. Majiyar ta shedamana Yaron na goye da wanda suka harba a kafa suna Asibiti don kulawar Likitoci.
Al'ummar garin Dandume sun shiga Damuwa da tashin hankali sosai ganin irin wannan rashin imani da 'Yan Bindigan suka nuna.