Saudiyya Tayi Alƙawarin sanya Hannun jari a Matatun Man Najeriya da Garambawul na musayar kuɗaɗen Kasashen Waje

top-news


A taron Saudiyya da Afirka da aka yi a birnin Riyadh, Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman, Yayi alƙawarin saka hannun jari wajen Gyara matatun man Najeriya tare da bayar da tallafin kudi domin ci gaba da sauye-sauyen canjin Kuɗaɗen waje da Gwamnati keyi.

Yarima mai jiran gadon ya kuma bayyana noma da makamashi mai sabuntawa a matsayin wuraren da Saudi Arabiya ta sanya hannun jari a Najeriya, Don taimakawa kasar ta sami isasshen abinci da makamashi, bi da bi.

Yarima bin Salman yayi nuni da cewa kamfanin mai na ƙasar Saudiyya, Saudi Aramco ne zai jagoranci zuba hannun jarin Matatun man a Najeriya, Inda za'a kammala aikin a cikin Shekaru biyu Zuwa uku.

Yarima Mai jiran Gadon ya kuma yaba da irin Rawar da Najeriya ke takawa wajen Tallafawa Kungiyar OPEC+.

KBC Hausa News

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *