Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da samun kuɗi Nera Biliyan biyu domin Tallafawa Al'umma da kayan Abinci
- Katsina City News
- 24 Aug, 2023
- 666
Hassan Abubakar Ahmad Katsina, Katsina Times
A ranar Laraba ne gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da samun Naira biliyan biyu daga cikin Naira biliyan 5 da gwamnatin tarayya ta amince wa jihohi.
Dakta Bala Salisu Zango, Kwamishinan yaɗa Labarai, Al’adu da harkokin cikin gida na jihar Katsina ne ya bayyana hakan a lokacin da yake mayar da martani game da jita-jitar cewa gwamnatin tarayya ta saki Naira biliyan 5 ga jihar.
Ya ce: “An jawo hankalin gwamnatin jihar kan labaran da ke yawo a kafafen yaɗa labarai na cewa gwamnatin tarayya ta saki Naira biliyan 5 ga jihohi domin sayen kayan Abinci." Yace
"Ina so in bayyana cewa, gwamnatin jihar Katsina ta samu Naira biliyan 2 kacal domin siyan hatsi da za a raba wa 'yan jihar".
Malam Salisu Zango ya ce kawo yanzu gwamnatin jihar ta yi amfani da Naira biliyan 2 wajen siyo buhunan Shinkafa 40,000 domin rabawa masu ƙaramin karfi a daukacin rumfunan zaɓe a faɗin jihar.
Ya ce gwamnati za ta kuma yi amfani da kaso na gaba na asusun, daga gwamnatin tarayya wajen siyan masara domin rabawa ga magidanta da suka cancanta.
Ya yi gargadin cewa gwamnatin jihar za ta ladabtar da duk wanda aka samu da ha'inci a aikin raba kayan agajin.