Aminu Balele Kurfi, ya raba kayan jinkai ga Al'ummar Mazabarsa na Dutsinma da Kurfi.
- Katsina City News
- 31 Oct, 2023
- 883
Zaharaddeen Ishaq Abubakar
A wani yunkuri na rage radadi da samar da Aikin yi ga Matasan Dutsinma da Kurfi, Danmajalisar mai wakiltar Kananan Hukumomin ya samar da Motocin Bus (Sieana) 10 da Keke-napep guda 43, Magunguna marasa lafiya ga Asibitocin yankin da tsabar kudi miliyan 15 don Tallafawa Dalibai.
A cikin jawabinsa Honorable Dan'Arewa yace "Da yardar Allah, a farkon watan sabuwar shekara mai kamawa Dan'Arewa zai kaddamar da rabon kudi ga marasa lafiya a duk wata amma ga wadanda ke kwance Asibitin mazabunsa na Kurfi da Dutsinma.
Yace "Dan'Arewa ba maganar Aikin (Project) na Miliyan dari yake a shekara ba, yana zancen Aikin (Project) na Miliyan dari biyar ne." Yace don haka wannan somin taɓi ne a ckin kasa ga wata biyar, duk a cikin sabuwar shekara za'aga linkin abinda yafi wannan."
Gwamnan Katsina Malam Dikko Umar Radda ne ya kaddamar da bada kayayyakin inda ya yaba da irin aikin jinkai na abokinsa Aminu Balele Dan'Arewa kamar yanda ya fada.
Gwamnan yace, wannan Gwamnatin tasu sunanta Babu cuta babu cutarwa, duk dan Siyasar da yayi da kyau zaiga da kyau, wanda kuma yaga akasin haka zaiga abinda ya shuka.
Gwamnan ya kara da cewa, kada wani mai muƙamin siyasa ya dauki alkawarin da baya iya cikawa har a daukeshi makaryaci ya tabbatar da ya dauki abinda yasan zai iya.
Radda ya jaddada aniyarsa ta bada tallafi na kayan abinci da kudin cefana ga talakawa lokaci zuwa lokaci domin rage wahalar rayuwa da albashi na wata-wata ga Limaman juma'a Masu bi masu da Ladanai masu kiran sallah, haka zalika yace suma masu unguwanni ba za amanta dasu ba za'a cigaba da basu albashi domin karamasu karfin gwiwa.
Gwamnan jihar Katsina yaja kunnen masu bangar siyasa inda yace su zama na gari, su zamo masu da'a su zo a koya masu sana'a su daina yawace yawace maras amfani, idan har sunji kuma sun bi, za aka karbesu hannu biyu, idan kuma sunki kuma suka saba doka, yace to akwai yanda za'ai dasu.
Taron da ya gudana a Sakatariyar Karamar hukumar Kurfi ya taro manyan 'Yan Siyasa na jihar Katsina da wakilan Majalisar tarayya.