Sauya Kidan Bakandamiyar Shata 1967
- Katsina City News
- 28 Oct, 2023
- 913
Dokta Aliyu Ibrahim Kankara PhD
Sai watarana cikin 1967 ana yaki lokacin mawakin na gyaran otel din Giva palace' (duba Babi na 12 domin cikakken bayani) a nan Funtuwa Sasuwai ya yi bajintar da ta kara ma mawakin waní tazara a tsakanin mawaka.
A lokacin kuma ana yin dambe a Funtuwar harma Sasuwai yaje kallo, yana kuma lura da hannun makadan damben da irin salon kidansu.
Shata na waka ana dauka a kaset a cikin otel din sai Sasuwaí yana ta lissafi yana ta lissafi ko ya saka wani bakon salo koko 2 Can sai ya zabura ya jefa wani kida na wani dan dambe da ake ce ma Karas din Kure.
Irin dai kidan farko na tashin ko jinjina na wakar. Don ya lura wakar Bakandamiya na bukatar namijin kida saboda waka ce ta tsoratar da abokan waka.
Da jin haka sai Shata kamar an yi masa allurar yaki ya zabura ya sa hannu ya kifar da wani teburi da ke gabansa wanda aka dora rikodar daukar wakar a bisa, ya je gaban Sasuwai din ya na cewa: "eye, eye'.
Shi kuma Ya'u wazirin Shatan ya taso ya na yi ma Sasuwai din likon kudi. Da aka gama aka watse da mangariba Shata ya kira marokinsa Ibrahim Dannayari ya ce ya nemo Sasuwai.
Ya tafi ya nemoshi yazo. Shata ya ce masa "abin da ya sa na kira ka, wannan kidan kada ka sake ka manta da shi ka rike shí da kyau' Ya ce 'ai bai manta ba'.
Shatan ya ce Karya ka ke yi' Duk da haka dai mawakin bai yarda ba saboda kuma naci na son sai wakar ta je daidai da abinda ya ke so sai da ya sa Sasuwai ya dauko kalangunasa suka tafi dakin shi a nan cikin gidan shi aka kira ma'amsa aka dosa waka cikin daren nan, Su ne basu daina wakar A/o alo ba sai da asuba, don dai Shata ya tabbatas sabon kidan Bakandamiyar ya zauna.
A nan kuma sabili da wannan sabon salo ya ke cewa: Na fara kidan Bakandamiya wanda maza ke shakka.
Mun ciro wannan Labarin daga Cikin Littafin "Shata Mahdi Mai Dogon Zamani" na Dokta Aliyu Ibrahim Kankara PhD. 07030797630