Hukunci mai Tsanani yayi Sanadiyar Mutuwar Dalibin Makarantar Al-azhar Academy a garin Zaria.
- Katsina City News
- 21 Oct, 2023
- 907
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A wani Labari da Jaridar Katsina Times ta samu, ranar Juma'a 20 ga watan Oktoba Malaman Makarantar Al-azhar Academy dake Kofar gayan a Karamar hukumar Zaria sun hallaka wani Dalibinsu mai suna Marwanu Nuhu Sambo, mai shekaru 17 a sakamakon Mummunan Bugu da sukai masa saboda kin zuwa Makaranta.
Wasu shedun gani da ido daga Daliban Makarantar sun bayyanawa wakilinmu cewa, anzo da dalibin a gaban Assembly malamai sukai ta bugunsa tun ana kirga yawan bugun da ake masa har aka manta lissafi, a karshe malaman da shugaban makarantar suka tafi dashi wani waje suka cigaba da bugunsa suka cire masa hakora, don tsananin bugu, a karshe dalibin ya mutu.
Wasu Daliban Makarantar sun bayyana mana cewa, bugun dalibai a makarantar da sumar da su ba sabon abu bane ga malaman.
An kai gawar Dalibin a wani Asibiti da ake kira Aridha Clinic inda Iyayen Dalibin suka samu labarin abinda ke faruwa suka garzaya Asibitin Likitan ya tabbatar masu da cewa shi ba mara lafiya aka kawo masa ba, gawa aka kawo masa.
Mun tattauna da Iyayen Yaron sun tabbatar mana da faruwar Lamarin, haka zalika hukumar 'yansanda ta garin Zaria a Ofishin su na Fadar Sarki sun tabbatar da lamarin. Mun nemi jin ta bakin shugaban makarantar hakan bai yiyu ba, amma da zaran munji ta bakinshi zamu sanar.
Kamar yanda ake zargi, Al-azhar Academy tayi kaurin suna wajen irin wannan zalunci wanda da dama ansha zarge zarge akan makarantar daga ciki hadda na karya dalibai da Azabtar dasu ta hanyoyi da dama.